Mai shari’a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta haramta wa dan takarar APC na jihar Bayelsa takara a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, Cif Timipre Sylva.
Mai shari’a Okorowo ya yanke hukuncin cewa Cif Sylva da aka rantsar da shi sau biyu kuma ya yi mulki na tsawon shekaru biyar a matsayin gwamnan jihar Bayelsa zai saba wa kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) idan aka bar shi ya sake tsayawa takara.
Alkalin ya kuma bayyana cewa Sylva bai cancanci tsayawa takara ba a zaben watan Nuwamba mai zuwa domin idan ya yi nasara aka rantsar da shi, zai shafe sama da shekaru takwas yana mulki a jihar.
Dangane da lamarin Marwa da Nyako a Kotun Koli, Mai Shari’a Okorowo ya lura cewa wanda suka tsara kundin tsarin mulkin kasar sun bayyana cewa babu wanda ya isa a zaba a matsayin gwamna fiye da sau biyu kuma bangarorin da ke kara sun amince cewa an zabi Sylva sau biyu.
Ya kara da cewa kotun koli ta yanke hukunci a shari’ar Marwa da Nyako cewa babu wanda zai iya fadada kundin tsarin mulki ko kuma fa’idarsa, don haka idan aka bar Sylva ya tsaya takara a zabe mai zuwa, yana nufin mutum zai iya tsayawa sau adadin da ya ga dama.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa an shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/821/2023 a ranar 13 ga watan Yuni 2023, ta hannun dan jam’iyyar APC Deme Kolomo.
Source LEADERSHIPHAUSA