Kungiyar Matasan Kudu Maso Yamma (SWYF) ta bukaci shugaba Bola Tinubu kada ya nada wani tsohon gwamna mukamin minista a gwamnatinsa.
Shugaban kungiyar, Kwamared Funsho Ajimuda ne ya bayyana hakan, cikin sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Asabar.
Ya zargi tsoffin gwamnonin da lafta wa jihohinsu basuka.
Ya ce, “Kamar yadda ake ta yamididi cewa wasu gwamnoni da dama na ta neman mukaman minista da wasu mukamai. Babu komai a cikin hakan illa tsagoran son kai da son zuciya bayan da suka shafe shekaru takwas a matsayin gwamna amma sun bige da neman kujerar minista.
“Wannan kungiya na fatan za a yi watsi da wannan bukatar tasu. Yana cikin kundin tarihi cewa gwamnonin nan sun lafta wa jihohinsu basukan cikin gida da na waje.
“Wasu daga cikin tsoffin gwamnonin sun zama gwamnoni ne ba tare da wani tsari ba.
Sun samu damar da za su hidimta wa jama’arsu amma sai suka yi wasa da damarsu.”
Kungiyar ta nemi shugaban kasan da ya jingene batun nada tsoffin gwamnoni a matsayin ministoci.