Koma bayan na Super Eagles ya samo asali ne sakamakon rashin nasara da ta yi a gida a farkon wannan wata a wasan da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta doke ta da 1-0 a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta 2022.
Duk da kokarin hushe haushin su wajen doke CAR da ci 2-0 a Kamaru bai hana tawagar ta Gernot Rohr da rikitowa zuwa kas aba.
Najeriya dake rike da kanbin gasar Afirka har guda uku ta ci gaba da rike matsayin ta na biyar a Nahiyar, inda Senegal har yanzu ke matsayi na ɗaya a nahiyar kuma ta 20 a duniya, sai Tunisia ke biye ma ta a matsayi na biyu, amma ta koma ta 27 a duniya.
A halin da ake ciki, Belgium ta ci gaba da kasancewa ta daya a duniya duk da cewa ta yi rashin nasara a wasanni biyu a gasar UEFA Nations League.
Brazil ce ta biyu, yayin da Faransa ke gaban Ingila zuwa matsayi na uku. Italiya ita ma ta kara zuwa matsayi na huɗu, yayin Ingila din ken a biyar.
A wani labarin na daban shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya Amaju Pinnick ya bayyana cewa, nan gaba tawagar Super Eagles za ta yi wasannin sada zumunta har guda biyar da manyan kasashen da suka yi fice a duniyar tamaula.
Pinnick ya ce, suna shirin gudanar da wasannin ne gabanin gasar cin kofin kwallon duniya da Rasha za ta karbi bakwanci a badi.
Pinnick ya kara da cewa, sun mayar da mankali wajen ganin sun yi wasannin da kasashen da ke jan ragama a jadawalin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya.
Sannan kuma kasashen su kasance cikin wadanda suka samu gurbi a gasar kofin duniya a Rasha.
Tuni dai Najeriya ta tuntubi wasu daga cikin kasashen don ganin cewa sun amince a yi wasannin na sada zumunta kafin zuwa Rasha a badi.
Sai dai kawo yanzu ba a bayyana sunayen kasashen ba, amma daga cikin ‘yan wasan na Najeriya akwai masu burin ganin cewa, sun yi wasa da Ingila.
Najeriya dai ta samu nasarar doke Argentina da ci 4-2 a wasan sada zumunta da suka yi a ranar 14 ga wannan wata na Nuwamba.