Hukumomin kasar Sudan sun sanar da janye izinin da suka baiwa tashar talabijen ta kasar Qatar Al Jazeera.Indan aka yi tuni jim kadan da juyin mulkin soji na ranar 25 ga watan Oktoba a Sudan ,yan sanda sun kama wakilin tashar Al Jazeera da wasu manema labarai dake aiki a wannan kasa.
A jiya asabar ne Ministan yada labaren kasar ta Sudan ya aike da wasika da nufin sanar da shugabanin tashar cewa ,ba su da izinin ci gaba da aiki a wannan kasa,wata majiya na zargin tashar da nuna wani bidiyo da ga duk alamu zai iya tunzura jama’a ga tashin hankali.
A wani labarin na daban Shugaban gwamnatin sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ce sojoji za su fice daga harkokin siyasar kasar bayan zaben da aka shirya yi a shekara ta 2023.
A ranar 25 ga watan Oktoba, Burhan ya kafa dokar ta baci, ya hambarar da gwamnatin kasar tare da tsare Firaminista Abdalla Hamdok, matakin da ya kara dagula tsarin mulkin farar hula a Sudan.
Juyin mulkin dai ya haifar da tofin A tsine da daukar matakan ladabtarwa daga gwamnatocin kasashen yammacin duniya da Bankin Duniya, da kuma zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, abinda ya tilastawa Janar al-Burhan maida Firaminista Hamdok kan mukaminsa a watan da ya gabata a karkashin wata yarjejeniya da suka kulla.