Shugaban kasar Sri Lanka wanda ke fuskantar matsin lamba ya yi tayin raba madafun iko da ‘yan adawa a yau Litinin,a yayin da zanga zangar neman ya yi murabus ke ta’azzara sakamakon karancin abinci, makamashi da magunguna da ya addabi kasar.
A wata sanarwa, shugaban Sri Lanka Rajapaksa ya gayyaci dukkannin jam’iyyun siyasa dake majalisar dokokin kasar da su karbi mukaman ministoci da za a ba su, tare da goyon bayan kokarin lalubo mafita ga matsalolin da suka addabi kasar.
Ya jaddada cewa za a samu masalaha ga matsalolin da suka addabi kasar ne kawai ta hanyar dimokaradiyya, a yayin da dubban mutane ke zanga zanga ta bai-daya a birane, garuruwa da kauyukan kasar.
Dukkannin ministocin kasar sun yi murabus
Wannan matakin na shugaba Rajapaksa na zuwa ne bayan da dukkannin mabobin majalisar zartaswar kasar, banda Rajapaksa da yayansa Firaminista Mahinda Rajapaksa, suka mika takardun murabus dinsu a daren Lahadi.
A waje daya kuma, shi ma gwamnan babban bankin kasar, Ajith Cabraal wanda ya dade da nuna adawa da kudin tallafi daga asusun bada lamuni na duniya IMF ya sauka daga mukaminsa a Litinin dinnan.