Sojojin Sudan sun kashe wani mai zanga-zanga a jiya Lahadi a yayin da suke murkushe dubban masu zanga-zangar neman mulkin farar hula, lamarin da ya kai adadin da aka kashe tun bayan juyin mulkin da sojojin suka yi a bara zuwa akalla 79.
An kuma gudanar da zanga-zangar ta Lahadi a wurare da suka hada da garuruwan Atbara da Dongola da ke arewacin kasar, da kuma yankin Darfur da ke yammacin kasar.
A birnin Khartoum, jami’an tsaro sun toshe wasu muhimman gadoji tare da rufe titunan da ke kan hanyar zuwa fadar shugaban kasar, kamar yadda suka sha yi a tsawon watanni ana zanga-zangar da aka saba yi.
Masu fafutukar kare hakkin dan adam sun ce hukumomin kasar, a cikin ‘yan makonnin nan, sun kama wasu karin mutane 45 gabanin tattakin na ranar Lahadi.
Kungiyar likitoci masu zaman kansu ta ce akalla mutane 79 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a zanga-zangar adawa da juyin mulkin.