Shugaban Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Jean-Claude Kassi Brou yace Sojojin kasar Mali sun tabbatar da aniyar su ta dawo da mulkin dimokiradiya a cikin kasar.
Brou wanda ke cikin tawagar wakilan kungiyar ECOWAS da ta ziyarci Bamako bayan Kanar Assimi Goita ya karbe iko daga hannun gwamnatin rikon kwarya yace sabbin shugabannin Sojojin sun bayyana aniyar su ta gudanar da zabe a watan Fabarairu mai zuwa da kuma mika mulki.
Kungiyar ECOWAS da AU duk sun dakatar da Mali sakamakon juyin mulkin da sojojin kasar suka yi sau biyu a cikin watanni 9, yayin da Faransa ta dakatar da aikin hadin gwuiwa wajen yaki da yan ta’adda da suke yi da sojojin Mali a yankin Sahel.
Goita ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar mulkin soji ranar litinin domin jagorancin gwamnatin rikon kwaryar da zata shirya zabe, kuma tuni ya nada Choguel Maiga a matsayin sabon Firaminista.
Sojoji sun dai hambarar da tsohuwar gwamnatin farar hula a watannin da suka gabata al’amarin da ake ganin a kwai sa hannun kasashen ketare musamman faransa.
Kungiyar kasashen yammacin afirka sunyi tir da wannan mataki da sojoji suka dauka a kasar ta mali inda aka gabatar da zaman tattaunawa da gwamnatin sojojin amma sai dai bai samar wata sakamako mai muhimmanci ba.
Sai dai kuma yanzu ana iya cewa an samu babban cigaba sakamakon bayyanar wannan labari wanda ke nuna cewa sojoji a kasar ta mali suna da niyyar mika mulki a hannun farar hula.
Amma abinda ya zama abin tambaya shine, wa zasu mika wa mulkin kasar?