Sojojin Isra’ila sun harbe wani Bafalasdine har lahira bayan da yayi rigima tare da amfani da wuka har ya tare da raunata wasu ‘yan kama wuri zauna 3, ciki har da jami’an ‘yan sanda 2.
Da safiyar Lahadin nan ne aka yi wannan fito na fito da makamai a kofar Bab al-Silsila ta shigamasallacin al-Aqsa a gabashin Birnin Kudus da Isra’ila ta mamaye.
Kafofin yada labaran yankin sun ce mutumin da ya kai wannan hari, mazaunin sansanin ‘yan gudun hijira na Shuafat ne a Birnin Kudus, kuma sunansa Fadi Abu Shkheidem mai shekaru 42.
Wadanda suka samu raunin da suka hada da ‘yan sanda 2 suna asibiti ana yi musu magani, kamar yadda cibiyar kula da lafiya ta Hadassah ta bayyana a wata sanarwa.
Rahotani sun ce Bafalasdine ya yi amfani da wuka ne wajen rigimar.
A wani labarin na daban sojojin Isra’ila sun bude wuta kan Falasdinawa masu zanga-zanga da ke jifansu da bama-bamai kirar gida da aka hada su da kwalabe, tare da kona tayoyi daga bayan shingen iyakar zirin Gaza.
Sojojin Isra’ila sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa “daruruwan masu tayar da tarzoma sun taru a shingen kan iyakarsu da Gaza, dan haka suna daukar matakan da suka dace wajen tarwatsa su, idan kuma ya zama dole za su bude wuta.
Kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas da ke mulkin zirin Gaza ce ta kira zanga-zanga a ranar Asabar don tunawa da kona Masallacin Al-Aqsa da ke Kudus da aka yi shekaru 52 da suka gabata.