A ranar 25 ga watan oktoban wannan shekarar da muke ciki ne sojojin jamhuriyar muslunci na Iran suka samu nasarar dakile wani mummunan shiri da sojojin amurka suka shirya na sace wani jirgin ruwa makare da man fetur mallakin Iran din a tekun oman.
Bincike ya tabbatar da cewa jirgin ruwan yana kan hanyar sa ne ta zuwa kasar venezuela kafin sojin amurka su masa tara tara inda suka canja masa akala kuma sukayi yunkurin sake gabadayan man da jirgin ke dauke dashi.
Amma sai dai sojin jamhuriyar muslunci ta Iran sunyi hanzarin isa wajen inda suka ceto man daga yunkurin satar da amurkan tayi.
Shugaban kasar ta Iran Ayatullah Ibrahim Ra’esi ya yabawa sojin na Iran bisa wannan namijin kokari da sukayi.
A bangare guda kuma shugaba Ra’esi ya bayyana yunkurin satar na amurka a matsayin wani mummunan lamari wanda tarihi bazai mance dashi ba.
Shima a nasa bangaren ministan albarkatun man fetue na Iran din ya bayyan jinjina gami da godiyar sa ga sojojin jamhuriyar musulunci ta Iran din.
Tuni dai kafafen sada zumunta suka cika da wannan batu inda akafar sadarwa da twitter ak fito da hashtag din #lesson_learned or we continue?, ma’ana kun dauki darasi ko mu cigaba a wani salo da Iraniyawa suka fito dashi domin yima amurkan shagube.
Tuni dai a yau ranar 4 ga watan nuwamba miliyoyin Iraniyawa suka tuttudo bisa tituna domin tunawa da ranar da aka kori amurka daga Iran din inda Iraniyawan sukayi amfani da wannan dama domin jan kunnen amurkan bisa kokarin shigar musu hanci da takeya bangarori mabambanta.
Iraniyawan sun bukaci amurka taji da kanta kuma ta guji shiga sabgogin jamhuriyar musulunci ta Iaran din a domin fa idan ta shiga ba kyale ta za’ayi ba
Wannan lamari dai ba karamin zubar da kimar amurkan yayi ba a tsakanin kasashen duniya.