Yayin bude taron shugabannin, shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Ghana Nana Akufo-Addo yace ana bukatar su da su yanke hukunci bayan sauraron ba’asi daga tawagar wakilan da suka ziyarci Guinea, yayin da ya bukaci goyan bayan sauran shugabannin kasashen yankin 15 dake halartar taron.
Ministar harkokin wajen Ghana Shirley Ayorkor Botchwey wadda ta jagoranci tawagar da ta je Guinea tace shugababbin sojin na da hurumin gabatar da shirin mayar da mulki ga fararen hula, amma kungiyar ECOWAS ce zata yanke hukunci akai.
Ana kuma sa ran taron ya saurari bayanai daga tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wanda ke shiga tsakani wajen ganin sojojin da suka yi juyin mulki a Mali sun cika alkawarin da suka dauka na gudanar da zabe.
Juyin mulki dai a nahiyar afirka na samuwa sakamakon tsananin zalunci da shugabanni mafi yawancin kasashe a nahiyar sukeyi.