Shugaban sojin Sudan Janar Abdel Fatah al-Burhan ya bayyana sunayen sabbin ‘yan majalisar rikon kwaryar kasar bayan juyin mulkin da ya yi a watan jiya.
Wannan na zuwa ne makwanni biyu da Burhan ya rusa gwamnatin Firaminista Abdalla Hamdok wanda aka tsare tare da ayyana dokar-ta-baci a fadin kasar.
Kazalika sabon garanbawul din na zuwa ne kwanaki biyu gabanin wata gagarumar zanga-zanga da al’ummar kasar suka shirya gudanarwa domin nuna adawa da juyin mulki. na ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata.
A wani labarin na dabna kuma gwamnatin Benin a ranar Laraba 10 ga watan Nuwamba ta yi maraba da kadarorin sarauta kusan 30 da aka wawashe daga kasar dake yankin Afirka ta yamma a lokacin mulkin mallakar turawan Faransa fiye da shekaru 130 da suka gabata.
Jirgin dake dauke da dukiyar masarautar ya sauka ne da yammacin Laraba a filin jirgin saman Cotonou, inda daruruwan mutane suka taru don nuna girmamawa, da kuma bayyana farin cikinsu.
A karshen watan Oktoba katafaren gidan adana kayan tarihi Quai Branly dake birnin Paris yayi baje-kolin gwamman kayayyakin tarihi da dakarun Faransa suka kwaso daga kasar Benin a zamanin mulkin mallaka, wanda kuma ya zama karo na karshe da za a nuna kayayyakin tarihin a Faransa kafin a mayar da su ga kasar ta Benin.