Zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya gana da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a gidan da aka ware masa Defence House, Abuja.
Channels tv ta rahoto cewa daga cikin mahalarta taron, wanda ya gudana cikin sirri har da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan.
Sauran jiga-jigan da suka halarci taron sun ƙunshi, mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, Sakataren watsa labarai na APC ta ƙasa, Iyiola Omisore, da tsohon sakataren kwamitin kamfe, James Faleke.
Me suka tattauna a taron?
Jim kaɗan bayan karkare taron, shugaban jam’iyya mai mulki na kasa, Abdullahi Adamu, ya ce taron zama ne da aka saba na yau da kullum.
Amma bai faɗi abinda suka tattauna ba.
Wannan ganawa ta manyan masu faɗa aji a jam’iyyar APC mai mulki ya zo ne kwanaki biyu kacal bayan Tinubu ya dawo gida Najeriya daga ƙasar Faransa, inda ya shafe kusan wata ɗaya.
Ku saurari ƙarin bayani…