Shugaban kasar Israila Isaac Herzog ya fara ziyarar sa ta farko a kasar Daular Larabawa tun bayan da kasashen biyu suka kulla huldar diflomasiya.
Kamfanin dillancin labaran kasar yace shugaban ya gana da Yariman Abu Dhabi Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan a fadar shugaban kasa.Wannan ziyara na zuwa kasa da wata daya da Isra’ila ta gabatar da wani kunshin matakan karfafa gwiwa ga yankunan yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, bayan da Ministan Tsaron Kasar Benny Gantz a lokacin ya karbi bakuncin shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a ziyararsa ta farko cikin shekaru da dama.
A wani labarin na daban Isra’ila ta bayyana shirinta na gina karin gidaje sama da dubu daya da dari 3 don tsugunar da Yahudawa ‘yan kama wuri zauna a yankin yamma da tekun Jordanda ta mamaye.
Wadannan sabbin gidaje, kari ne a kan sama da gidaje 2000, wadanda majiyoyin tsaro suka ce za a ba mazauna cikinsu takardun izinin zama a yankin, lamarin da ya janyo caccaka daga Falasdinawa, masu fafutukar lalubo zaman lafiya da kuma makwafciyarta, Jordan.
A wata sanarwa, ministan samar da gidajen Isra’ila Zeev Elkin, wanda dan jam’iyyar New Hope party mai ra’ayin mazan jiya ne, ya ce jaddada kasancewar Yahudawa a yamma da kogin Jordan yana da mahimmancin ga manufofin akidar Zionism.
Da yake jawabi a taron mako mako na majalisar zartaswar Falasdinawa, Firaminista Mohammed Shtayyeh ya yi kira ga majalisar dinkin duniya da musamman ma Amurka da su tinkari Isra’ila a kan wannan mataki da take daf da dauka.
Kimanin Yahudawa dubu 475,000 ne suka share wuri suka zauna a Yamma da kogin Jordan, inda Falasdinawa ke kallo a matsayin makomarsu.