Shugaba Joe Biden na Amurka ya fuskanci mummunan koma-baya a fagen siyasa, bayan da majalisar dattawa ta yi watsi da shirinsa na yi wa dokar kada kuri’a a cikin majalisar gyara.Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Biden ke kokarin kare muhimman ayyukan da ya aiwartar a cikin shekara daya da ya share kan karagar mulki.
Wannan dai na tabbatar da cewa ‘ya’yan jam’iyyar Republican ne suka sa kafa suka yi fatali da wadannan sauye-sauye da shugaba Biden ya ce za su kara kyautata tsarin dimokuiradiyya a cikin kasar ta Amurka.
A sanarwar da ya fitar a shafinsa na twitter, shugaba Biden ya bayyana matukar damuwa a game da wannan koma-baya, to sai dai ya ce zai ci gaba da aiwatar da sauye-sauye da nufin karfafa dimokuradiyya a kasar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Joe Biden ke gabatar da taron manema labarai don fayyace wasu daga cikin muhimman ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar, da suka hada da yaki da cutar covid-19, samar da ayyuka ga Amurka da matakan da yake dauka don kawo karshen hauhawar farashin kaya a cikin kasar ta Amurka.