Shugaba Buhari zai tafi birnin Paris na kasar Faransa a ranar Lahadi, 16 ga watan Mayu, don taron Kasashen Afirka.
Shugaba buhari na Najeriya, tare da wasu daga cikin mukarraban sa masu fada a ji, za su kasance a Paris na tsawon kwanaki hudu.
A yayin ziyarar, shugaba Buhari zai gana da takwaransa na Faransa, Macron, domin tattauna batutuwan tsaro a yankin Sahel da sauran muhimman batutuwa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, 16 ga watan Mayu zai tashi daga Abuja zuwa Paris, Faransa, kan ziyarar aiki ta kwanaki hudu domin halartar taron Kasashen Afirka, fadar shugaban kasar ta sanar.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar a ranar Asabar, 15 ga watan Mayu, wacce Legit.ng ta hango a shafin Twitter ta nuna cewa taron zai mayar da hankali ne kan nazarin tattalin arzikin Afirka, biyo bayan firgita daga annobar COVID-19.
Shugaba Buhari ya shirya wata tafiya ta kwanaki 4 zuwa kasar waje Hoto: Femi Adesina Source: Facebook Za a duba yiwuwar samun sauki, musamman daga karin nauyin bashi da ke kan kasashe, a wajen taron, kamar yadda Legit.ng ta samu labari.
Taron wanda Shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai karbi bakuncinsa zai jawo hankalin manyan masu ruwa da tsaki a cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya da wasu Shugabannin Gwamnati, wadanda za su hada kai, su tattauna batun samar da kudade daga waje da kuma bashi ga Afirka, da kuma sake fasalin kamfanoni masu zaman kansu. Matsalar tsaro da za’a tattauna A yayin ziyarar,
Shugaba Buhari zai gana da Shugaba Macron don tattauna barazanar tsaro da ke ci gaba a yankin Sahel da Tafkin Chadi. Zai kuma tattauna kan alakar siyasa, alakar tattalin arziki, canjin yanayi da hadin gwiwa wajen siyan bangaren kiwon lafiya, musamman wajen duba yaduwar COVID-19, tare da karin bincike da allurar rigakafi.
Shugaba Buhari zai tarbi wasu manyan masu fada a ji a harkar mai da iskar gas, injiniyanci da sadarwa, Majalisar Tarayyar Turai da Wakilin Tarayyar Turai kan Manufofin Tsaro, da kuma yan Najeriya.
Membobin majalisar zartarwar da za su raka shugaban Legit.ng ta tattaro cewa shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin waje,
Geoffrey Onyeama, ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ministan kasuwanci da zuba jari, Otunba Adeniyi Adebayo, da kuma ministan lafiya, Dr E. Osagie Ehanire.
Har ila yau, a cikin ziyarar akwai mai ba Shugaban kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Babagana Mohammed Monguno (rtd) da kuma babban darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Amb. Ahmed Rufa’i Abubakar.
A wani labarin, kasar Isra’ila ta kai hari gidan benen da ofishin gidan jaridar AlJazeera, AP da wasu kamfanonin jaridar ke ciki a birnin Gaza, kasar Falasdin.
A bidiyon da Alarabiya ta dauka, an ga yadda makami mai linzami da Isra’ila ta harba ya rusa ginin har kasa. Mai ginin benen, Jawwad Mahdi, ya bayyana cewa hukumar Sojin Isra’ila ta kirashi cewa za’a kaiwa gidansa hari.