Shugaba , Muhammadu Buhari, ya sauka daga muƙamin shugaban NBA bayan ƙarewar wa’adinsa.
Shugaba Buhari yayi godiya ga dukkan shugabannin ƙasashen da NBA ta haɗa bisa goyon bayan da suka nuna masa na tsawon shekara biyar.
Yace a halin yanzu zai miƙa jagoranci ga sabon shugaban da aka zaɓa, ya roƙi sauran shugabannin su bada haɗin kai Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yayi kira ga ƙasashen duniya da su taimaka wajen ƙoƙarin da ake na kawo cigaba a yankin tafkin Niger, wurin da ya kasance matsugunin mutane Miliyan 160m, waɗanda suka dogara da rafin domin tafiyar da rayuwarsu.
Buhari ya faɗi haka ne yayin da yake buɗe taron shugabannin ƙasashen da tafkin Niger (NBA) ya haɗa karo na 12 a Abuja ranar Alhamis, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Legit.ng hausa ta gano cewa, Taron ya gudana ta hanyar amfani da fasahar zamani (Virtually).
Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da mai taimakawa shugaban ta fannin yaɗa labarai, Femi Adesina, ya fitar mai taken “Shugaba Buhari ya nemi ƙasashen duniya su taimaka wajen haɓaka tafkin Niger.”
Shugaba Buhari yace tafkin na bada gudummuwa sosai wajen noma, kiwon kifi, kiwon dabbobi da dai sauran su, kamar yadda punch ta ruwaito.
A matsayin shugaba wanda wa’adinsa ya ƙare a hukumar NBA, shugaba Buhari yace: “Yan uwana shugabanni, Abun alfahari ne gareni da na jagoranci taron shugabannin ƙasashe na tsawon shekara biyar da suka wuce, tun sanda kuka amince dani a taron mu karo na 11 daya gudana a Cotonou, Benin ranar 8 ga watan Janairu, 2016 in jagoranci abinda ya haɗa mu (NBA).”
“Daga cikin matakan da muka ɗauka a NBA, Shirin samar da kuɗaɗe ga NBA 2016-2024 ne kaɗai bamu kammala gudanar da shi ba.”
“A wannan taron, wa’adina a matsayin shugaban NBA yake cika, zan miƙa jagoranci ga sabon shugaban da aka zaɓa. Ina roƙon ku da ku baiwa sabon shugaba haɗin kai yadda ya kamata domin kawo cigaba a wannan yanki da ya haɗa mu.”
A wani labarin kuma Jami’an Kashe Wuta Sun Ceto Rayuwar Mutum 197 da Dukiyoyin Miliyan N75m a Jihar Kano Hukumar kashe wuta ta jihar Kano ta bayyana cewa ta samu nasarar ceto rayukan mutane 197 a watan Mayu, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Tace ta kuma ceto dukiyoyi na kimanin miliyan N75m a lamarin kashe wuta 68 da ta samu a faɗin jihar.