Shugaba Muhammadu Buhari ya ce tun da aka dawo da mulkin dimokaradiyya a shekarar 1999, babu gwamnatin za ta kwatanta kanta da tasa a wajen dawo da Najeriya hayyacinta.
Tsohon shugaba kasar, Olusegun Obasanjo ne ya fara mulki tun da dimokaradiyya ta dawo a shekarar 1999, kana ya mika wa Umaru Musa yaradua a shekarar 2007.
Yar’adua bai karasa wa’adin mulkinsa ba sakamakon rashin lafiya, kuma bayan ya mutu a shekarar 2010 ne Goodluck Jonathan, wanda shine mataimakinsa ya karasa wa’adin mulkin Yaradua, ya kuma dora tasa a shekarar 2011, har zuwa lokacin da Buhari ya buge shi a shekarar 2015.
A jawabinsa ga al’ummar Najeriya, Buhari ya ce abin takaici ne ganin yadda masu adawa suka gaza fahimtar ci gaban da aka samu a gwamnatinsa.
A wani labarin na daban majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ayyana ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane da kuma hare-hare cikin kasar a matsayin ‘yan ta’adda.
A baya bayan nan ne dai cikin watan Satumban da ke shirin karewa gungun ‘yan bindiga masu yawan gaske suka kai wani mummunan hari kan sansanin sojoji da ke Burkusuma a Karamar Hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto ta Najeriya, inda ake fargabar sun halaka jami’an tsaro fiye da 10.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne da safiyar Juma’a a kauyen Dama da ke karamar hukumar ta Sabon Birnin.
‘Yan ta’addar sun kuma kai wani harin kan kauyen Katsira, inda nan kuma suka hallaka mutane hudu.
A karshen watan Satumba, wasu majiyoyin sojin Najeriya suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mayakan Boko Haram fiye da akalla 250 da suke biyayya da tsohon jagoransu Abubakar Shekau, sun fice daga sansaninsu da ke arewa maso gabashin kasar zuwa arewa maso yammaci, domin hada karfi da ‘yan bindiga a dajin Rijana da ke jihar Kaduna.
A cewar daya daga cikin majiyoyin gungun mayakan na Boko Haram ne suka kitsa wasu sace-sacen da ake yi a arewa maso yammacin Najeriya a baya bayan nan, yayin da kuma suke ci gaba da horas da ‘yan bindiga wajen sarrafa manyan bindigogin harbo jiragen sama, bama-bamai da sauran muggan makamai.