Ya ce al’ummar kasa ita ce karfin iko, ba kujerar da mai iko yake zaune a kanta ba, ko kuma jami’an tsaro da sojoji da soji da suke kare shi a kan wannan kujera ba.
Domin kuwa a cewar sheikh Isa Kaseem, duk mai mulkin da al’ummarsa ba su tare da shi, shi kansa ba zai taba jin dadin mulkin nasa ba.
A kan haka ya ce, yin aiki tare da kowane bangare na al’ummar kasa ba tare da la’akari da banbacin akida ko addini ko ra’ayin siyasa ba, shi ne zai hada kan al’ummar kasar baki daya, kuma shi ne zai ba mahukuntan kasar natsuwa, rashin hakan kuma shi ne zai sanya su zama cikin zullumi da tsoron jama’a
A wani labarin na daban shafin jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, a jiya Allah ya yi wa Mahmud Abdulsattar al-Atwi makarancin kur’ani kuma mahardaci rasuwa bayan samun matsalar bugun zuciya a kauyen Shabanat da ke lardin Shaqiyyah a kasar Masar, wanda ya rasu yana da shekaru 26 a duniya.
Muhammad Abdulsattar mahaifin Mahmud Abdulsattar ya bayyana cewa, dansa yana daga cikin matasa masu tarbiya ta addini da kuma riko da kur’ani mai tsarki a cikin rayuwarsa.
Ya ce dansa ya kasance tun daga lokacin kuruciyarsa, yaro ne mai son addini mai riko da kyawawan dabi’u da girmama na gaba, da kuma son zama da malamai.
Da farko dai ya fara da koyon tilawa, inda ya shahara a kauyensu da kyakyawan sautinsa na karatun kur’ani, daga bisani kuma ya shiga harda kur’ani inda ya kammala harda a cikin kankanin lokaci.