Sheikh Alwazin ya kirayi zaman taron ne a bangaren koyar da ilimin kur’ani na jami’ar Diqhaliyya a kasar Masar, da nufin yin bayani na fadakawrwa ga daliban ilimi.
A cikin bayanin nasa ya yi ishara da yadda wasu daga cikin masu karkatacciyar fahimta kan kur’ani da sunnar manzo (SAW) da ma adinin kansa suke yin amfani da karkatacciyar fahimtarsu kan ayoyin kur’ani da sunnar ma’aiki wajen saka matasa cikin ayyukan ta’addanci da sunan jihadi.
Sheikh Alwazina yace wannana bu ne da ya kamata a gyara shi ta hanyar fadakarwa, kuma nauyi ne a matakin farko da ya rataya kan malaman addini da hukumomi na kasashen musulmi.
Kasar Masar dai a halin yanzu tana daga cikin kasashen larabawa da ake samun karuwar masu tsatsauran ra’ayi na Salafiyya, wadanda galibi su ne suke shiga kungiyoyin da ake kira na jihadi da suke kaddamar da ayyukan ta’addanci da sunan jihadi.
A wani labarin na daban yau ne kwamitin da ke kula da shirya tarukan makon hadin kan musulmi na duniya ya fara gudanar da zamansa tare da halartar dukkanin mambobi.
Shugaban kwamitin Mahdi Agha Muhammad ne ya sanar da hakan a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna, inda ya bayyana cewa, zaman taron na farko da aka fara an tattauna yadda zaman zai kasance a wannan shekara.
A shekarar bara saboda matsalolin da ake ciki na bullar cutar korona, an gudanar da taron ne kai tsaye ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo, inda masu gabatar da jawabai suka rika gabatar da jawansu da makaloli kai tsaye.
Ya ce har yanzu wanann batu yana daga cikin abin da yke ci wa al’ummomin duniya tuwo a kwarya, a kan haka sun fara tattaunawa kan yadda taron na bana ya kamata ya kasance, duk kuwa da cewa ba a yanke shawara guda kan hakan ba, amma za a ci gaba da tatatunawa domin samun matsaya guda.
Kwatin da ke daukar nauyin shirya tarukan hadin kan musulmi na duniya dai yana karkashin cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya ne, da ke da babban ofishinta a birnin Tehran.
Marigayi Imam Khomenei ne ya kirkiro makon hadin kan musulmi musulmin duniya, wanda ya sanya makon haihuwar manzon Allah a cikin watan watan rabi’ul Awwal ya zama shi ne makon hadin kan musulmi na duniya baki daya.