An kwashe tsawon shekaru dai ana ta bin kadun wannan shari’ar, wadda aka yi ta jan kafa a kanta saboda dalilai na siyasa.
Zaman sauraren shari’ar da yake farawa daga yau 7 ga watan satumba, zai ci gaba har zuwa ranar 17 ga wannan wata, inda Khalid Sheikh Muhammad zai gurfaa, tare da Walid Muhammad saleh Mubarak, Ali Abdulaziz Ali, Ramzi Bin Shaibah, da kuma Musatafa Ahmad Adam Hausawi.
Hukumar FBI ta kasar Amurka ta sheda cewa, kusan dukkanin bayanan da ake da su na tuhumar wadannan mutanen, tabbatattun bayanai ne, domin kuwa kusan dukkanin abin da ke ciki su ne da kansu suka yi bayani, baya ga sauran abubuwa wadada suka dogara a kan bayanan sirri da kuma shedu na mutane da kuma na hotunan bidiyo da daisauransu.
Majiyoyin kungiyar Taliban sun kungiyar ta kammala kwace iko da jihar Panjshir a kasar Afhanistan, bayan dauki ba dadi da mayakan kungiyar suka yi da magoya bayan Ahmad Mas’ud, wanda yaki mika kai ga kungiyar.
A cikin wani bayani da kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya yi ga mayakan kungiyar a cikin filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Kabul, ya bayyana cewa, an kawo karshen yaki a kasar, kuma sun shimfida ikonsu a jihar Panjshir wadda taki mika wuya.
Baya ga haka kuma kungiyar ta nuna hotunan bidiyo na babban ginin gwamnatin jihar Panjshir, inda mayakan kungiyar suka saukar da tutar kasar Afghanistan da ke wurin, suka dora tutarsu.
Sai dai a nasa bangaren Ahmad Mas’ud wanda ke jagorantar mayakan yankin na Panjshir wajen yin turjiya a gaban mayakan Taliban tare da kin mika wuya gare su ya karyata cewa Taliban ta kammala kwace iko da jihar baki daya.
Haka nan kuma ya yi ikirarin cewa, sunan nan cikin jihar kuma za su gaba da yaki da Taliban, kamar yadda ya bukaci al’ummar Afghanistan da su mike su kwaci ‘yancin kansu daga mulkin mallakar Taliban.