Dan Bola Ahmad Tinubu, Seyi ya fito a gangamin da aka gudanar a jihar Kano, inda aka ga taron matasa magoya bayan APC.
Gwamna Ganduje ya ce Kano jihar Tinubu ce, kuma tabbas zai kawo jihar a zaben da za a gudanar a watan Fabrairun 2023.
Ba wannan ne karon farko da jinin dan takarar shugaban kasa zai fito fili don shiga gangamin zabe ba.
Seyi, da ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya dura jihar Kano a ranar Lahadi domin jagorantar dandazon masoya mahaifinsa a wani gangamin tallata jam’iyyar.
Daraktan tawagar kamfen Tinubu/Shettima, Baffa Babba Danagundi ya yi bayani game da wannan lamari, inda yace wannan gangami zai yi kira ne ga masoya Tinubu da su tabbatar sun mallaki katin zabe kafin 2023.
A hotunan Legit.ng Hausa ta gani daga jaridar The Nation, an ga dandazon jama’a a birnin Kano, lamarin da ya yi sanadiyyar hana wasu masu kasuwanci a yankin tafiyar da lamuransu.
An tattaro cewa, wannan gangami da APC ta yi ta shirya gangamin mutane miliyan daya masu katin zaben PVC ne a jihar Kano.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya hallara a wannan gangami, ya kuma bayyana cewa, an yi taron ne don nuna goyon baya ga dan takarar da ‘yan APC za su zaba a zaben Fabrairun 2023, DailyPost ta ruwaito.
A cewarsa: “Mun shirya wannan gangamin mutum miliyan daya masu PVC ne domin nuna cewa jihar ta Tinubu ce.”
Mubarak Munkaila, matashi dan jam’iyyar APC a jihar Kano da aka gudanar da wannan gangami tare dashi ya shaidawa wakilin Legit.ng Hausa cewa, ya ji dadin ganin yadda dan takarar shugaban kasan ya turo dansa irin wannan gangami.
A cewarsa: “A baya da wahala ka ga dan dan siyasa a cikin matasa ‘ya’yan talakawa suna yawo a rana da sunan kamfen, yanzu kuma mun ga bambanci, dan Tinubu ne ya jagorance mu.
“Za mu yi mahaifinsa a 2023 ba tare da la’akari da kudi ba, ba ma bukatar komai, kawai yadda ya nuna yana yinmu matasa shi ya burge mu.”
A wannan shekarar, ‘yan siyasa na damawa da ‘ya’yansu a lamuran da suka shafi kamfen, musamman a wasu bangarori da matasa ke iya bi.
Source:Legithausa