Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba ya bayyana sauya shekar gwamnan Kross Riba, Ben Ayade, zuwa jam’iyar All Progressives Congress (APC) ya girgizasu kuma yayi matukar basu kunya.
Gwamna Ishaku ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban ma’aikatar Aso Rock, Farfesa Ibrahim Gambari ranar Juma’a, rahoton DT.
Ishaku yace: “Ba san abin yake tunani ba, saboda mun yi matukar girgiza da fitarsa daga jam’iyyarmu zuwa APC, saboda dukkanmu na ganin PDP matsayin mafita daga APC.” “Kuma dukkan gwamnonin PDP na kokari sosai a jihohinsu.
Amma ban san dalilin da ya sa ya Sauya sheka zuwa APC ba.” Gwamnan yace wannan ba laifin kwamitin sulhu da dinke barakar jam’iyyar karkashin Saraki bane saboda mambobin kwamitin sun yi kokarin ganin cewa bai sauya sheka ba.
“Sun yi kokari sosai. Amma ya danganta da shawarar da mutum ya yanke ko abinda yake sa ran samu,” yace.
A wani labarin na daban dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Bruno Fernandez ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kungiyar na shekarar bana na wanda yafi kowa kokari a kungiyar a kakar bana mai karewa.
Karo na biyu kenan a jere da dan wasan ke lashe wannan kyauta duk da cewar a watan Janairun shekara ta 2020, ya kulla yarjejeniya da Manchester United daga kungiyar Sporting Lisbon ta Portugal.
Cikin sanawar da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, Manchester United ta ce Bruno Fernandez ya lashe kyautar gwarzon nata na bana bayan samun mafi rinjayen kuri’un da magoya bayan kungiyar suka kada daga kasashe fiye da 200, abinda ya bashi nasarar doke dan wasan gaaba, Edinson cabani da kuma Luke Shaw.
A wannan kakar wasa, kwallaye 18 gwarzon na Manchester United ya ci cikinsu har da guda 9 a gasar Europa, ya yin wasanni 36 da ya buga kuma har yanzu ba’a kammala buga wasan kakar bana ba.
A ranar Lahadi Manchester United zata fafata da kungiyar kwallon kafa ta Woberhampton a wasan kungiyar na karshe sannan kwanaki uku tsakani ta buga wasan karshe na cin kofin Europa League da billareal a birnin Gdansk na kasar Poland.