Sarkin Kano na 14 Muhammad Sanusi II, ya kalubalanci dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, da rashin amincewa da shan kayen da aka yi masa a zaben gwamnan Kano na 2023.
Lamido ya bayyana hakan a wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta na zamani, tsohon Sarkin magana kan da yadda ‘yan adawa suka shigar da kara a kotun sauraren karar zaben gwamnan Kano har zuwa kotun koli, har suka kai ga shan kaye a kotun koli, wanda hakan ke nuna karara ga Gawuna cewa bai karbi rashin nasarar faduwa zaben ba tunda farko sai daga baya.
Sarki Sanusi II,y a jaddada hakkin ‘yan kasa na zaben shugabannin da suka zaba. Ya yi Allah-wadai da matakin hana ‘yan kasa zabin da suka zaba bayan sun kada kuri’unsu, yana mai cewa hakan ya saba wa tsarin dimokuradiyya.
Sanusi ya ce, “Bayan da mutane suka kada kuri’a suka fadi zabe, sai suka garzaya kotu domin karbe mulki da karfi, sai suka gamu da hukuncin Allah a kotu ta karshe, sai kawai suka ce sun yi imani da hukuncin Allah.”
Sarki Sanusi ya bukaci kowa da kowa ya yi koyi da yadda ‘yan adawa suka amince da shan kaye tare da karfafa karfin gwiwa wajen fuskantar hukuncin shari’a.
Kazalika, Sanusin ya yi wa gwamnan Kano addu’a da nasiha kan ya tausayawa mutanen jihar ya yi musu aiki da ya kamata.
Source: LEADERSHIPHAUSA