Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, yace idan har za’a yi adalci kudu ne ya kamata ta karbi mulkin kasar nan a 2023 Ortom, ɗaya daga cikin tawagar G5, yace tun farko gwamna.
Wike ya dace ya gaji Buhari a PDP amma wasu maƙiya suka murɗe Gwamnan ya halarci gangamin taron kaddamar da kamfen PDP reshen jihar Ribas a Patakwal.
Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, yace maganar gaskiya ɗan kudu ya kamata ya gaji kujerar shugaban ƙasa bayan shugaba Buhari ya sauka a 2023.
A rahoton Channels TV, Ortom ya bayyana haka ne a filin wasan Adokiye Amiesimaka yayin kaddamar da yakin neman zaɓen PDP a Patakwal, jihar Ribas.
A wurin gangamin taron, Gwamna Ortom ya bugi kirjin cewa shi ne gwamnan arewa na farko da ya goyi bayan kudancin Najeriya ta karɓi mulki.
Nyesom Wike Ortom, ɗaya daga cikin gwamnonin PDP biyar da suka matsa lamba sai Ayu ya yi murabus, yace maida mulki kudu shi ne adalci da dai-daito.
Yace: “Yan Najeriya, ku sani domin tabbatar da adalci da dai-daito ku tsammani mulki ya koma kudu bayan shugaba Buhari ya karkare shekaru Takwas hakan ne ya dace a yi.”
“Mu ‘yan Najeriya ne bisa haka ya wajaba a kanmu mu tabbatar mun yi aiki a dunkule cikin haɗin kai.”
Wa ya kamata Buhari ya miƙa wa mulki?
Gwamnan Benuwai ya ƙara da cewa takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike ne ya cancanci ya gaji shugaban ƙasa Buhari amma, “Wasu maƙiyan cigaba” suka yi ruwa suka yi tsaki ya sha kaye a zaɓen fidda gwani.
Punch ta ruwaito Ortom na cewa: “Ɗanku daga nan Ribas ya nemi takara aka ce wai ya sha kaye amma wasun mu sun yi imanin cewa shi ya dace ya haɗa kan ƙasa, ga ja kowa a jiki kuma ya tabbatar an yi wa kowa adalci.”
“Ina fatan mutanen mu a Ribas su yi wa gwamnan mu Nyesom Wike aiki, daga ƙarshe zamu yanke matsayarmi ta karshe kamar dai G5 saboda Najeriya ta shiga tsaka mai wuya sai tashi tsaye zasu ceto ta.”
A wani labarin kuma Gwamna Wike, tawagar gwamnonin G5 da wasu ƙusoshin jma’iyyar PDP sun shiga ganawa a jihar Legas.
Bayanan ɗa muka samu sun nuna cewa taron manyan kusoshim PDP ba zai rasa alaƙa da kokarin tsige shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu ba gabanin 2023.
An ce taron wanda ke gudana yanzu haka, zai tattauna kan wasu karin ci gaba da aka samu a PDP da kuma duba matakin da zasu ɗauka na gaba.
Source:Legithausa