Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo da kuma tsofaffin gwamonin jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, Mohammed Ahmed Makarfi da Ramalan Yero, sun lashi takobin fatattakar jam’iyyar APC daga jihar.
Sun sanar da hakan ne a jawabinsu daban-daban a lokacin kaddamar da yakin neman zaben dan takarar PDP na Kaduna ta Tsakiya da sauran ‘yan takarar PDP a jihar.
Sambo a matsayinsa na bako na musamman a wajen taron, ya yi kira ga daukacin ‘yan jihar da su fito kwan su da kwarkwatar don zabar ‘yan takarar PDP a zabukan 2023,
Shi kuwa Yero da Sanata Makarfi, sun yi nuni da cewa, akwai bukatar ‘ya’yan PDP su hada kansu waje guda ba tare da nuna wata wariya ta mazabu ba don a samar wa da PDP kuri’u masu yawa a lokacin zabukan da za a shiga.
Su ma a nasu jawabin, Sanata Shehu Sani, Sanata Musa Bello, ya yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da kuma daukacin al’ummar Jihar Kaduna da su tabbatar da sun yi amfani da kuri’unsu don korar jam’iyyar APC daga kan mulki.
A wani labarin na daban kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, ya ce dan takararta na shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso zai kayar da abokan hamayyarsa da kuri’u miliyan uku a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kwamitin ga bayyana hakan ne a ranar Litinin cikin wata sanarwa da Cif Precious Elekima, Kodinetan Kudu Maso Kudu na kwamitin ya fitar.
A cewar kwamitin, Rabi’u Kwankwaso zai yi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa domin tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya za su iya zabar shugabanni masu nagarta da kima.
Kwamitin na Kwankwaso ya kuma ce ba gaskiya ba ne cewa jam’iyyar za ta mara wa wani dan takara baya.
Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya nagari da su zabi mutumin da ya shahara da amana da gaskiya wanda zai ceto Nijeriya.
Source:LegitHausa