A wannan Juma’ar ce dai Hukumar Sadarwar Najeriya NCC ta fitar da sanarwar dake fadakar da miliyoyin masu amfani da na’urorin Komfuta da kuma wayoyin hannu dangane da barazanar muguwar manhajar ta Flubot a Najeriya.
Hukumar ta NCC ta ce ta samu bayanai kan barazanar ce daga kwamitin kar ta kwana dangane da lamurran na’ura mai kwakwalwa na Najeriya kan cewa manhajar ta Flubot na kai hari kan wayoyin hannu na Android da sauran dangoginsu ta hanyar fakewa da kokarin baiwa bayanan mutane kariya ko kuma tallata musu sabbin manhajoji.
A cewar daraktan hulda da jama’a na NCC, Dakta Ikechukwu Adinde, Flubot ana kwaikwayon aikace -aikacen manhajojin hada-hadar banki da wayoyin hannu na Android ke amfani da su, sai dai burinsa shi ne satar bayanan mutane da kuma sace kudaden dake asusunsu na bankuna idan ya samu dama.
A wani labarin na daban gwamnatin Amurka ta tabbatar da rahoton cewa an yi mata kutse a hanyoyin sadarwar na’urorita, bayan da jaridar ‘The Washinton Post’ ta ruwaito cewa akalla ma’aikatun kasar 2 masu kutse daga Rasha suka kai wa farmaki.
Kamfanin na FireEye ya ce yana zargin wata kasa ce ta dau nauyin wannan kutse.
Kakakin hukumar tsaron kafar intanet na Amurka, ya ce suna aiki sau da kafa da abokan huldar hukumomin kasar a game da kusten da aka gano wasu sun yi wa hanyoyin sadarwar gwamnati.
Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa hukumar tsaron FBI na binciken wasu kungiyoyi da ke aiki da hukumar leken asirin kasa da kasa ta Rasha, suna mai cewa an shafe tsawon watanni ana wannan kutse.
Sai dai ofishin jakadancin Rasha a Amurka ya mayar da martani cikin fushi, inda ya nesanta kansa da al’amarin kutsen, yana mai cewa labarin kanzon kurege ne daga kafafen yada labaran Amurka, kuma manufofinta da fahimtar ta na huldar kasa da kasa sun yi hannun riga da hakan.