Jam’iyyar APC a jihar Filato ya bayyana jin dadinta da yadda rikicin cikin gida ke kara dabaibaye jam’iyyar adawa ta PDP.
Wata kungiyar jam’iyyar PDP mai goyon bayan Atiku ta barranta da tsohon gwamnan jihar, David Jonah Jang.
Gwamna Nyesom Wike na ci gaba da bayyana adawarsa ga shugabancin jam’iyyar PDP, lamarin da ke kara kunno rikici a jam’iyyar.
Jam’iyyar APC a jihar Filato ta bayyana cewa, karin rikicin gida da jam’iyyar PDP ke fuskanta alheri ne gare ta saboda hakan zai kara kaimin nasararta a zaben 2023 mai zuwa.
Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar goyon bayan Atiku a Filato mai suna Plateau for Atiku Movement (PAM) a ranar Talata ta yi taron ‘yan jarida don nuna barranta da tsohon gwamnan jihar.
Kungiyar ta bayyana rashin goyon bayanta ga Jonah David Jang ne bisa zargin ya koma tsagin gwamna Nyesom Wike mai adawa da Atiku.
Gwamna Wike na ci gaba da bayyana adawarsa ga dan takarar shugaban kas ana jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar tare da neman a tsige shugaban PDP na kasa Iyochia Ayu.
A taron da kungiyar ta gudanar tare da jagorancin Istifanus Mwansat ta ce, Jang ya basu kunya wajen juyawa Atiku baya tare da bin sahun Wike. Mun ji dadi, ba mu ji dadi ba.
A bangarenta, APC ta ce hakan ya yi mata dadi, inda sakataren yada labaranta Sylvanus Namang yace nan gaba kadan mambobin PDP za su samu rabuwar kai.
A cewarsa: “Jang ne mamallakin PDP saboda tsarin komai shi ke tafiyar dashi. Saboda haka, don sun nuna rashin goyon bayansa hakan zai dagula lamari ne kawai.
Ba zan ce mun ji dadin haka ba saboda muna son abokan hamayya masu karfi, amma ta wata hanyar muna jin dadi saboda za mu nasara cikin sauki.”
Shugabannin wata kungiyar PDP sun koma APC Ana cikin irin wannan yanayin, wasu jiga-jigan PDP suka bayyana komawar su jam’iyyar APC mai mulki saboda wasu dalilai nasu.
Wannan na zuwa ne jim kadan bayan fara gangamin kamfen na zaben 2023 da dukkan jam’iyyun siyasar suka fara a watan jiya.
Source:Legithausa