Rigakafin cutar Korona ya rage karfin yaduwar ta da kashi 40 cikin 100, a cewar Hukumar lafiya ta duniya ranar Laraba, tana mai gargadin cewa mutane su kiyayi abin da zai jefa su cikin hatsarin kamuwa da ita.
Tedros ya lura da cewa a makon da ya gabata, fiye da kashi 60% daga cikin 100% na daukacin rahotannin da aka yada kan mace macen da ake samu yanzu, a sanadiyar cutar ta Korona yafi karfi a kasashen Turai
Shugaban ya ci gaba da cewa, karuwar adadin da aka samu a wannan karon baya rasa nasaba da karancin matsin lamba, kan tsarin kiwon lafiya da kuma gajiyawar ma’aikatan wannan bangaren.
Ya kara da cewar duk wanda ya yi allurar rigakafin yana da kariya daga kamuwa da cutar ta Korona, amma wannan ba zai hana shi kiyaye wa daga sakaci da ka iya sanya wa a kamu da ita ba.
Sai dai wadannan bayanai na shugaban hukumar lafiya ta duniya ya sanya shakku sosai da sosan gaske dangane da ingancin rigakafin korona din a zukatan mutane sakamakon yadda aka fahimci cewa rigakafin baya bada kariya dari bisa dari daga annobar cutar ta korona.
A wani labarin na daban kuma hukumar lafiya ta duniya ta ce tana bibiyar sabon nau’in cutar Covid 19 na Delta sau da kafa don tantace ko yaduwarsa ta kai ta ainihin cutar, a daidai lokacin da adadin wadandan cutar Covid-19 ke harbewa ke karuwa a duniya.
Hukumar tana ci gaba da nazari ko garkuwar dan Adam tana turje wa wani nau’in cutar da ake kira AY.42, wanda aka gano a kasashe 42 na duniya.
Masana cututtuka masu yaduwa a hukumar na gudanar da bincike don tantance ko akwai sauyi a yanayin yaduwar wannan nau’in cuta, ko kuma wani nakasu a garkuwar jikin dan adam wajen yaki da kwaryar cutar.
Alkalumman da mujallar kimiyya ta GISAID ta dora a shafinta na nuni da cewa kaso 93 na wadanda aka gano suna dauke da sabon nau’in cutar duk a Birtaniya suke.
Hukumar ta WHO ta kara da cewa, a rabe-raben masu kamuwa da sabon nau’in cutar, an samu karuwar masu dauke da cutar a tsakanin wadanda shekarunsu ba su kai 25 ba tun farkon watan Yuli, musamman a yankunan Turai da yammacin Pasifik.
Hakan, ta ce ba ya rasa nasaba da cewa dattawa ne aka fi yi wa rigakafi, ko kuma matasa ne suka fi cudanya da juna babu shamaki, duba da yiwuwar cewa cutar na yaduwa a makarantu ganin yadda matasa suka koma daukar darasi.