Kamfanin Pfizer ya yi ikirarin cewa sabon nau’in rigakafin Covid-19 na kwaya da ya samar na da tasirin yakar cutar da akalla kashi 89. Acewar kamfanin ikirarin nasa ya biyo bayan jerangiyar bincike da kuma gwaje-gwajen da ya aiwatar kan kwayar rigakafin.
Kamfanin na Pfizer da hadin gwiwar BioNTech na matsayin kan gaba a jerin kamfanonin magunguna 8 da suka samar da rigakafin cutar ta covid-19 wadda zuwa yanzu ta kashe mutane fiye da miliyan 5 a sassan duniya, ya zama kamfani na biyu bayan Merck na Amurka da ya yi ikirarin samar da rigakafin na kwaya.
Acewar kamfanin na Pfizer nau’in rigakafin nasa na kwaya mai suna Paxlovid zai taimake gaya wajen magance cutar, hana kamuwa da ita dama rigakafinta.
Kamfanin wanda ya bayyana samar da nau’in kwayar rigakafin a matsayin babbar nasara ga duniya baki daya la’akari da yadda cutat ke ci gaba da kisa ya yi ikirarin cewa nau’in kwayar zai taimaka wajen rage cunkoson da asibitoci ke gani a kokarin karbar allurar rigakafin.
Acewar kamfanin yanzu haka yana shirin mikawa hukumar kula da abinci da magunguna ta Duniya nau’in kwayar don kammala bincike tare da sahale fara amfani da shi.
A wani labarin na daban hukumar Lafiya ta duniya WHO ta sahale fara amfani da nau’in rigakafin corona na Covaxin da kamfanin Bharat Biotech na India ya samar bayan gwajinsa tare da gano tasirinsa a yaki da cutar wadda zuwa yanzu ta hallaka mutane fiye da miliyan 5 a sassan Duniya.
Nau’in rigakafin na Covaxin shi ne irinsa na farko da aka samar tare da yin gwajinsa cikin kasar India kuma WHO ta sahale amfani da shi inbanda sauran rigakafi da kamfanonin magani na kasar ke taya aikin samar da su.
Acewar hukumar ta WHO nau’in rigakafin na da sahihancin kashi 78 wajen yaki da cutar ta covid-19 bayan gwajin allurarsa sau bibbiyu kan jama’a cikin makwanni 4 da suka gabata.
WHO ta bayyana cewa nau’in rigakafin na Covaxin zai yi tasiri hatta a kanana da matsakaitan kasashe la’akari da saukinsa wajen adanawa da kuma dadewar da ya ke gabanin lalacewa.
Nau’in rigakafin na India ya zama rigakafi na 8 da zuwa yanzu Duniya ke amfani da shi don yakar cutar bayan Pfizer da BioNTech da Moderna da AstraZeneca da Johnson and Johnson baya ga Sinopharm da Sinovac.