Kamfanin BUA ya bayyana yadda ‘yan kasuwa da dillalai ke gallazawa ‘yan Najeriya a harkallar siminti, ta hanyar dora ribar da ta wuce ka’ida.
Ya bayyana haka ne bayan ganawa da shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja, inda ya koka kan farashin na siminti.
Ya bayyana cewa, dillalai da ‘yan kasuwa ne ke cin kazamin ribar data wuce kima, inda suke samun kusan N1000 kan kowane buhu.
Wani rahoton Daily Trust ya bayyana cewa, kamfanin simintin BUA ya ta’allaka ci gaba da hauhawar farashin siminti a kasar ga ‘yan kasuwa da ke cin kazamin riba fiye da kima a harkallar siminti a kasar. Kamfanin ya zargi ‘yan kasuwa da taka rawar gani wajen ganin farashin siminti bai sauko ba a Najeriya, lamarin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa a kai.
Shugaban kamfanin, Abdul Samad Rabiu ne ya bayyana haka a lokacin da ya gana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ya ziyartar shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya ce kamfanin na kan tattaunawa da sauran masu sana’ar sarrafa siminti don rage farashin siminti a Najeriya, inda ya ce:
“Idan ba ka da goyon bayan dukkan abokan harkalla, hakan ba zai yiwu ba.” ‘Yan kasuwa da dillalai ke cin kazamin riba.
Da yake ta’allaka laifin tsadar simintin ga ‘yan kasuwa, shugaban na BUA ya ce, kamfaninsa ya samar da wani ragin farashi, amma sauran kamfanoni basu yi koyi da hakan ba. Hakazalika, ya ce ‘yan kasuwa suna samun akalla ribar N800 zuwa N1000 kan kowane buhu, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
“A gaskiya mun yi tunanin ta hanyar rage N350, sauran kamfanoni za su yi koyi da haka. Hakan bai faru ba. Kuma muna ganin yanayin da har yanzu farashin siminti na sama, kun san haka, dillalai da ‘yan kasuwa suna samun ribar kusan Naira 800 zuwa N1000 kan kowane buhu.”
A wani labarin, rikici tsakanin kamfanin BUA da na sukarin Dangote ya zama mai girma a masana’antar sukari, kuma alamu na nuna tafiyar ta fi karbar BUA wanda ya zargi kamfanin sukarin Dangote kwanan nan da son haifar da karancin sukari.
A cinikayyar ranar Laraba, 23 ga Fabrairu, 2022, farashin hannun jarin kamfanin sukarin Dangote ya ragu da 5.28%, inda kasuwa ta rufe yana da Naira 17.05 kan kowane hannu, farashin kasuwarsa ya sauka kenan daga Naira biliyan 218 zuwa Naira biliyan 207.10.
Kamfanin sukarin ya sami raguwar farashin hannun jari, kuma za a iya danganta shi da sauyin ra’ayin masu zuba hannun jari wanda ya haifar da sayar da hannayen jari a kamfanin kan kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya.