Akwai yiwuwar Real Madrid ba za ta samu sayen ɗan wasan gaba na Borussia Dortmund Erling Haaland ba saboda alamu sun nuna cewa zai koma Manchester City ko kuma Paris St-Germain. (AS – in Spanish)
Barcelona na son ta sha gaban Real Madrid wajen sayen ɗan wasan gaban PSG da Faransa Kylian Mbappe inda kwantiragin ɗan wasan mai shekara 22 zai ƙare a kaka mai zuwa. (AS – in Spanish)
Manchester United da Chelsea na da ra’ayin ɗan wasan gaban na Norway mai shekara 21, wanda zai buƙaci albashin sama da fam miliyan 30 a shekara. (ESPN)
Everton na son sayen ɗan wasan tsakiyar Manchester United da Ingila Jesse Lingard mai shekara 28 a watan Janairu. (Football Insider)
A wani labarin na daban kungiyar kwallon kafa ta PSG ta sanar da kammala sayen dan wasan baya na Inter Milan Achraf Hakimi wanda ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru 5 da kungiyar ta Faransa.
Kafin rattaba hannu kan kwantiragin dai akwai jita-jitar da ke cewa Hakimi mai shekaru 22 na shirin komawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tare da Marcos Alonso.
Cikin kakar wasan da ta gabata, Hakimi ya zura kwallaye 7 a wasannin da ya dokawa kungiyar ta sa ta Inter Milan wanda ya bata damar dage kofin Serie A, karon farko bayan shekarar 2010.
Matashin dan wasan bayan ya faro kwallonsa da Real Madrid ko da ya ke ta bayar da shi aro har na shekaru 2 ga Borussia Dortmund gabanin komawa Inter a 2020, yayinda a yanzu ya sake sauya sheka zuwa Faransa.