Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya musanta da kakkausar murya kan rattaba hannu kan wata yarjejeniya da fadar shugaban kasa kafin ranar 12 ga watan Janairu, 2024 don neman kotun koli ta tabbatar da shi a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kano.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, kan wata takarda da ke karade shafukan sada zumunta wacce ke nuni da amincewar Gwamnan kan rattaba wasu kuduri hudu tsakaninsa da fadar shugaban kasa gabanin nasarar da ya samu a kotun koli, a matsayin karya.
“Domin jan hankali da nanatawa, kan yarjejeniyar karya da ke cewa, Gwamna Yusuf ya amince ya sauya shekar jam’iyyarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, zai ruguza masarautun jihar biyar ko kuma ya barsu, zai dakatar da ruguza gine-ginen da basu halatta ba, sannan zai kafa majalisar dattawan Kano. Wannan zance ne mara tushe.
“Gwamnan na son ya bayyana karara cewa, kasancewar ya samu nasarar lashe zabensa ta hanyar kuri’un jama’ar Kano kuma hukuncin kotun koli ya sake tabbatar da nasararsa, don haka, babu wani dan siyasa da zai yi masa bazarana.
“Bari in sake tunatar da ‘yan siyasa da ke fakewa a karkashin inuwar shugaban kasa cewa, duk wata shawara ko alkiblar siyasa da za a bi a Kano, za a tabbatar da ita ne a cikin tsarin doka da ikon zartarwa da kundun mulkin Nijeriya ya tanadarwa ofishin Gwamna.
“Mun karyata wannan jita-jita, kuma mun bayyana cewa, babu wani tofe da karairayi da za su dauke hankalin mai girma Gwamna, Abba Kabir Yusuf wajen gabatar da ayyuka da shirye-shiryensa na habaka jihar kano da al’ummarta.” inji sanarwar.
Source: LEADERSHIPHAUSA