Kakakin fadar gwamnatin rasha Kremlin Dmitry Peskov ya caccaki Amurka dangane da matsin lamba kan yuwuwar sake mamayar da Rasha ke yi a Ukraine, bayan da kasashen yammacin duniya suka zargi Moscow da jibge karin sojoji kusa da tsohuwar tarayyar Soviet.
Peskov ya bayyanawa gidan talabijin na kasar rasha cewa, bai kamata Amurka da itama ke da sojoji a yankin da matsa lamba kan al’amuran da suka shafi kasarsu ba.
Tun a shekarar 2014 ne sojojin kasar Ukraine ke ci gaba da gwabza kazamin fada da ‘yan aware masu goyon bayan Rasha a yankuna biyu da ke kan iyaka da Rasha, bayan da Moscow ta mamaye yankin Crimea daga Ukraine.
Kiev da kawayenta na Yamma suna zargin Rasha da aika dakaru da makamai a kan iyakar kasar domin tallafa wa ‘yan aware – sai dai Moscow ta musanta.
A wani labarin na daban shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Rasha Vladimir Putin na ganawa Laraban nan, a haduwarsu ta farko tun bayan da Biden ya hau karagar mulki, to sai dai babu tsammanin cimma jituwa tsakanin bangarorin biyu masu banbancin ra’ayi.
Amurka da Rasha na takaddama kan batutuwa da dama, kama daga batun takaita mallakar makamai da kutse ta hanyar intanet, da batun kutsen zabe da kuma lamuran da suka shafi Ukraine.
Babu fatan samun nasara
Wani babban jami’in Amurka ya fadawa manema labarai a cikin jirgin Air Force One yayin da Biden ya tashi zuwa Geneva, yana mai cewa ana sa ran za su tattauna na tsawon awanni hudu ko biyar da misalin karfe 11: 30 agogon GMT, to sai dai yace, basa tsammanin wani sauyi.
Yayin da shima mai baiwa shugana Putin shawara kan harkokin kasahen waje Yuru Ushakove yace “Bashi da tabbas ko za’a cimma matsya da kuma kulla wata yarjejeniya ba.”
Tsamin dangantaka
Dangantaka ta tabarbare tsawon shekaru tsakanin kasashen biyu, musamman mamayar da Rasha ta yi wa yankin Crimea dake Ukraine a shekarar 2014, Amurka ta kuma zargi Rasha da shiga yakin Syria a shekarar 2015 – wanda Moscow ta musanta – sai kuma batun tsoma bakinta a zaben 2016 wanda ya kawo Donald Trump Fadar White House.
Kasashen biyu sun kuma nunawa juna yatsa a karkashin jagorancin Biden na baya-bayan nan a watan Maris, lokacin da kira Putin “mai kisan kai”, matakin da ya sa Rasha ta sake kiran jakadanta da ke Washington komawa gida, yayin da itama Amurka ta kira jakadanta a watan Afrilu.