Sakamakon abubuwan da suke ta faruwa da sauye-sauyen da ake samu a cikin sauria kasar Afghanistan bayan da Taliban ta kwace iko da mulkin, wannan ya sanya kasashen duniya musamman manya ciki kuwa har da kasar rasha bayyana matsayarsu a halin yanzu kafin amincewa da mulkin Taliban.
Wannan yana zuwa ne bayan da shugaban na Taliban Mulla Baradar ya koma birnin Kabul daga birnin Doha, inda yake ganawa da sauran bangarori na kungiyar Taliban da kuma na jama’a gami da ‘yan siyasa da kungiyoyi daban-daban.
Yanzu haka dai dubban ‘yan kasar ta Afghnistan ne suka tsere wasu kuma suna shirin tserewa tun bayan da Taliban ta kwace iko da kasar, inda UAE ta ce ya zuwa ta kwashe ‘yan Afghanistan dubu 8 da 500 daga kasarsu, kuma za ta tsugunnar da dubu 5 daga cikinsua cikin kasarta.
A nata bangaren kasar Rasha ata bakin ministan harkokin wajen kasar, rasha tana ci gaba da tattaunawa da Talibana kan batutuwa daban-daban, amma kuma hakan ba yana nufin amincewa da ita ba ne.
Sergey Lavrov ya ce amicewa da Taliban a hukumance yana dogara da yadda kamun ludayinta ya kasance ne a nan gaba.
A daya bangaren kuma dubun-dubatar ‘yan kasar Afghanistan mazauna birnin Landan na kasar Burtaniya, sun bazana kan tituna suna rera take yin tir da kwace mulki da Taliban ta yi a kasar Afghanistan.
Baya ga haka kuma ‘yan kasar ta Afghanistan da suke gudanar da zanga-zangar, sun yi Allawadai da matakin da kasashen turai suka dauka na nuna rashin katabus, inda suke bayyana cewa akwai hadin bakin kasashen turai a cikin abin da ya faru, msamman ma Amurka da Burtaniya.