Rahotanni sun bayyana yadda wani jariri ya tsira daga harin Isra’ila wanda ta kai yankin Gaza.
Rahotanni sun nuna cewa Israila Ta Ruguje Gini Ta Kashe Uwa da ‘Ya’yanta 4 a Gaza cewa, mahaifiyar jaririn da ‘yan uwansa sun mutu yayin da gini ya ruguje a kansu.
Isra’ila na ci gaba da kai hari kan al’ummar Falasdinawa dake zaune a Gaza, lamarin ya yi sanadiyyar rasa rayuka Rahotanni daga gabas ta tsakiya sun bayyana cewa an garzaya da wani jaririn Bafalasdine zuwa asibiti bayan tsinto shi a cikin wani ruguzajjen gini da Isra’ila ta lalatawa Falasdinawa a yankin Gaza.
Hukumomin lafiya na Gaza sun ce wani makami da Isra’ila ta harba ne ya ruguza katafaren ginin, ya kuma kashe mahaifiyar yaron da ‘yan uwansa hudu a birnin na Gaza.
Jaririn mai suna Omar Al-Hadidi ya raunata ne a hannunsa da kafarsa amma ana yi gaggauwar masa magani.
Rahotanni sun nuna cewa jaririn ne a karkashin gini kasan inda mahaifiyarsa ta rasu, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Rikici na ci gaba da ta’azzara tsakanin Falasdinawa da jami’an tsaron Isra’ila inda ake ta luguden wuta, lamarin da ya jawo asarar rayuwaka da dama, musamman na Falasdinawa dake zaune a yankin Gaza.
Rikici tsakanin yankin Falasdinu da Isra’ila rikici ne da ya shafe shekaru ana yinsa, wanda kawo yanzu ya kai ga kashe adadin mutane mai yawan gaske.
A wani labarin, Dubun-dubatar masu zanga-zanga sun yi jerin gwano zuwa ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Landan don kira ga daukar matakin gaggawa daga gwamnati don kawo karshen mummunan muzgunawa da ake yi wa Falasdinawa a rikicin Gaza.
Rikicin na Gaza ya tilasta wa dubban Falasdinawa barin gidajensu saboda yawan asarar rayuka da dukiyoyi.
Jaridar Punch a baya ta ba da rahoton cewa Shugaba Recep Erdogan na Turkiyya ya yi kira ga Shugaban, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), da ya ba da hadin kai ga Falasdinawa bayan sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai wa Kudus da Gaza.
Cikin hadin kai, dubban mutane sun fito kan titunan Landan don rera taken “‘Yanta Falasdinu” don nuna adawa da rikicin Gaza.