Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya gana da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
An ba Obi shawarin ya hada kan ‘yan Najeriya idan ya gaji Buhari a zaben 2023 mai zuwa nan da watanni biyu.
Peter Obi ya samu goyon bayan tsoffin shugabannin Najeriya, ciki har da Olusegun Obasanjo yayin da suka gana.
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya gana da tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan a gidan da ke birnin Yenagoa a jihar Bayelsa.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, an ce Obi da Jonathan ya can suna wata ganawar sirri gabanin fara gangamin kamfen na LP a jihar Bayelsa, Channels Tv ta ruwaito.
A fahimtar Jonathan, Najeriya na cikin matsanancin halin rabuwar kai, ya shaidawa Obi cewa, idan ya samu nasara a zaben 2023 ya fara da hada kan Najeriya.
Hakazalika, ya yaba wa Ono bisa daukar matakin tsayawa takara a zaben na badi kuma a jam’iyyun APC ko PDP ba.
A tafiyar Obi zuwa gidan Jonathan, yana tare da abokin takararsa, Yusuf Baba-Ahmad da wasu jiga-jigan jam’iyyar, rahoton Vanguard. Karbuwar Obi a idon tsoffin shugabanni da jiga-jigan kasar nan.
A watan Satumban da ta gabata, tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga tafiyar Peter Obi.
Hakazalika, ya gana da tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalam Abubakar mai ritaya a gidansa da ke jihar Neja a watan na Satumba.
Obi na ci gaba da fadada tafiyar gangamin kamfensa da habaka tallata manufofinsa gabanin babban zaben 2023 da ake fuskanta nan da watanni biyu masu zuwa.
A wani labarin kuma, wani fitaccen malamin addini ya bayyana cewa, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ne zai ci zaben 2023.
Satguru ya bayyana hakan ne yayin bikin cikarsa shekaru 75 a duniya, inda yace Tinubu ne yake da halayen da suke da kyau na zama shugaba.
Hakazalika, ya ce Atiku ba zai lashe zaben badi ba saboda yana da kabilanci da nunawa wariyar addini a fannin siyasa.