A makon nan ne gwamnan jihar Anambra, farfesa Chukwuma Soludo ya nuna baya goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi.
Gwamnan ya rubuta doguwar takardar da ya bayyana matsayarsa da cewa, Peter Obi ba zai yi nasara ba a zaben 2023.
Maganar Soludo dai ta jawo cece-kuce, inda dansa, Ozinna ya bayyana ra’ayin mai bambanci da mahaifins a.
Ozonna Soludo, dan gwamnan jihar Anambra ya bayyana ra’ayinsa kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023 mai zuwa.
Matashin mai shekaru 28 da ke zaune a Burtaniya ya yi tsokaci a shafin Facebook kan wani rubutu da ke caccakar mahaifinsa da ya ce Peter Obi ba zai ci zabe a 2023 ba.
A ranar Litinin 14 ga watan Nuwamba, Farfesa Soludo ya ce sam Peter Obi ya san ba zai ci zabe ba, kawai dai yana takara ne a zaben mai zuwa.
Tonon Sililin da Gwamnan Anambra Ya Yi Wa Peter Obi Ya Tsokano Masa Fushin ‘Obidients’
Gwamnan na Anambra ya kuma yi zargin cewa, talauci da fatara karuwa suka yi a Anambra a lokacin mulkin Obi.
Peter Obi: Ra’ayin Soludo da dansa sun saba kan batun dan takarar LP
‘Yan a mutun Obi sun caccaki Soludo
Wannan lamari dai ya haifar da cece-kuce a shafin sada zumunta, mutane da dama ‘yan a mutun Obi sun caccaki gwamnan na Anambra.
Yayin da ake ta kokarin jawo dan Soludo, Ozonna cikin lamarin, shi kuwa ya fito ya bayyana ra’ayinsa sabanin na mahaifinsa.
“Zan zo ba a tsoma ni cikin wannan ba. Ni ba na kan ra’ayin kowa. Ina da nawa ra’ayin kuma a kullum ina tunanin Peter Obi ne dan takara mafi cancanta. Duk wannan bani da alaka dashi.”
‘Obidients’ sun fusata bayan da Soludo ya yiwa Obi tonon silili
A tun farko kun ji cewa, gwamna Soludo ya yiwa Peter Obi tonon silili kan kasuwancin da ake cewa ya habaka a jihar Anambra lokacin da yake gwamna.
Soludo ya fito a gidan talabijin ne, inda ya yi kaca-kaca da jarin kasuwancin da ake cewa Obi ya gina a jiharsa.
Maganganun da Soludo ya yi sun fusata ‘yan a mutun Obi, inda suka yi ta maganganu masu zafi kan gwamnan mai ci na Anambra.
Source:LegitHauasa