Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka kammala a ranar 25 ga watan Fabrairu, kuma jam’iyyarsa za ta tabbatar wa duniya cewa ta yi nasara.
Obi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wani taron manema labarai a Abuja.
Dan takarar jam’iyyar LP, wanda ya bayyana a bainar jama’a na farko tun bayan zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, ya ce zaben ya gaza cimma mafi karancin ma’auni na gudanar da zabe mai inganci, don haka zai tunkari kotu domin kwato kujerarsa.
Peter Obi ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar LP da magoya bayansa a kasar nan da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’a a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da za a yi a ranar 11 ga watan Maris mai zuwa a fadin kasar.
A wani labarin na daban Alhaji Nasiru Gawuna, mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, ya taya zababben shugaban kasa, Sanata Bola Tinubu, da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, murnar nasarar da suka samu a zaben ranar Asabar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Malam Hassan Musa-Fagge ya fitar a ranar Laraba a Kano.
Gawuna ya kuma yabawa magoya bayan jam’iyyar da suka bayar da ruwan kuri’unsu ga ‘yan takarar jam’iyyar, ya sake yin kira gare su da su sake fitowa su kada kuri’unsu a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da za a yi a ranar 11 ga watan Maris.
“Kun fito a baya kuma mun yi imanin za ku sake yin hakan a cikin tsarin siyasa na zaman lafiya don tabbatar da nasarar ‘yan takararmu masu neman mukamai daban-daban a jihar” in ji shi.
Source:LeadershipHausa