Dan takarar shugaban kasa na 2023 a jam’iyyar labour party ( LP) Mista Peter Obi ya bayyana cewa bai bar jam’iyyar ba.
A kwai rade radin cewa Peter Obi ya raba gari da jami’iyyar tasa, amma dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa alakar sa da jami’iyyar har yanzu tana nan, ya kuma bayyana cewa wannan rashin dai dai din daga bata gari ne.
Peter Obi media watch (POMR) a ta bakin babban mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Obi- Datti, Dr Yunusa Tanko yace sun fito fili suyi watsi da labaran karya da ake yadawa na cewa Obi zai fice daga jam’iyyar, yace wannan magana ba gaskiya bace kuma ba ta samo asali daga Obi ko Obidient Movement ba.
Sai dai daga ‘yan barna ne wadanda suka dukufa sai sun haifar da rigima a cikin jam’iyyar inji Tanko, ya kara da cewa ba yau aka fara tafka kura kurai a jam’iyyar ba.
A halin yanzu kudurin mu shine samar da Najeriya mai Inganci ba tare da bangaranci ba, siyasa ta kare tun ranar 26 ga Oktoba 2023 lokacin da kotu ta yanke hukuncin ta a kan babban zaben kasa.
Wadanda suka himmatu wajen haifar da rikici a jam’iyyar labour party, a fili take makiya ne ga ci gaban dimokoradiyyar dake halin ha’ula’i a Najeriya.
A halin yanzu abinda Obi ya sa a gaba shine ganin yadda za’a gudanar da mulkin dimokoradiyya bisa ka’idojin da aka ayyana, ba bisa wariyar launin fata ko kuma duk wani halin rashin adalchi da ya yawaita a yanzu a kasar nan ba.
Duba Nan: Sanata Shehu Sani Ya Nuna Damuwa Kan Furucin Wani Malami
Tanko ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya musamman masu ra’ayin Obidient cewa Obi yana nan a labour ba tare da girgiza ba kuma gwagwarmayar ceto ‘yan Najeriya ba zata tsaya ba har sai an kai gaci ta hanyar amincewar ‘yan Najeriya.