Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta yi tir da harin da ƴan daba suka kai ofishin Sanata Barau Jibrin.
Hakan na cikin wani saƙon murya da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar Bashir Sanata ya aike wa
A cikin saƙon Sanata ya zargi jam’iyyar APC da yunƙurin dawo da siyasar daba a Kano.
Ya ci gaba da cewa, ya kamata APC ta sani an riga an wuce irin wannan siyasar.
Ya ce “A lokacinmu mun samarwa matasa aikin yi saboda bamu yarda da irin wannan tsarinba, amma yanzu ana ƙoƙarin mayar da Kano baya”.
Ya ƙara da cewa “Matasan nan da su muke alfahari, idan ka gina su ka gina al’umma, amma idan wasu ƴan siyasa na amfani da matasa domin daba to hakan ba zai haifar mana ɗa mai ido ba”.
Labarai masu alaƙa:
Ba a kama Abdullahi Abbas ba – APC tsagin Ganduje
Mahawarar cikin jam’iyyar APC a Kano tsagin Gwamna da tsagin Shekarau
A wannan makon mai ƙarewa ne jam’iyyar APC tsagin tsohon Gwamna Malam Shekarau suka zargi ɓangaren Gwamna Abdullahi Ganduje da kai wa ofishin yaƙin neman zaɓen Sanata Barau Jibrin hari.
Sai dai tsagin Gwamna Ganduje ya musanta wannan zargi.
Rundunar ƴan sandan Kano ta ce ta cafke wasu matasa 13 bisa zargin wannan farmaki, tare da gurfanar da su a gaban kotu.