Shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar yace tabbas ya amince jam’iyyar PDP ta tafka kuskure Gwamna Udom Emmanuel yace duk da haka.
PDP zata lalubo inda ta yi kuskure kana ta gyara kafin babban zaben 2023 Babbar jam’iyyar hamayya ta ƙasa PDP na fama da rigingimu a cikin gida musamman kan batun G5.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, yace jam’iyyar PDP zata warware rigingimun cikin gida da suka hanata zaman lafiya gabanin 2023.
Gwamna Emmanuel, shugaban kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na PDP, ya faɗi haka ne yayin hira da jaridar This Day.
Da yake bayyana kwarin guiwar kawo karshen taƙaddamar cikin gida a PDP, gwamnan yace kowace kuri’a ɗaya tana da muhimmanci idan har jam’iyyar na fatan lashe zaɓe mai zuwa.
“Muna kokarin lalubo hanyar da zata bulle mana ne, shiyasa baku da aiki sai tambayar halin jam’iyyarmu ke ciki.
Ina faɗa muku mun samu cigaba, komai zai wuce ba zamu yi hasarar kowa ba, muna son kowace kuri’a.”
“Kowa na da muhimmanci ba wai manyan jiga-jigai ba. Su ɗin (G5) da kuke gani bani da matsala da su, suna tare da jam’iyya, ko sun gaya muku sun fusata da PDP?
Huɗu daga cikinsu suna rike da tikitin PDP.”
“Ko Cokali da Faranti suna faɗa da junansu har kaji ƙara ta tashi amma hakan ba yana nufin sun kareraye bane.
Kamar haka ne ke faruwa, jam’iyya mafi girma a Afirka ba zaka rasa ta da kunji-kunji ba.”
Mun tafka kuskure amma mu zamu ci zaɓe – Emmanuel
“Saboda haka a zahirin gaskiya mun yi kuskure, na amince da haka, a jam’iyya mun tafka kuskure, a ɗai-ɗaikun mu mun yi kuskure amma ina tabbatar muku kuskuren ba zai raba mu ba.” – Udom Emmanuel.
Gwamna Emmanuel ya ƙara da cewa jam’iyyar PDP ce zata ci zaɓen 2023 kuma da ace ya san jam’iyyar ba zata kai labari ba, ba zai karɓi shugabancin kwamitin kamfe ba.
A wani labarin kuma Matasan Katsina Sun Yi Wa Atiku Alkawarin Kuri’u Miliyan Shida a Zaben 2023 Matasan Katsina karkashin ƙungiyar magoya bayan Atiku Abubakar, sun yi taron rantsar da Kodinetocinsu na ƙananan hukumomi 34 dake sassan jihar.
A wurin taron wanda ya gudana a babban Ofishin kamfen shugaban kasa na PDP, matasan sun sha alwashin kawo wa Atiku kuri’u aƙalla miliyan Shida a zaɓe mai zuwa.