Jam’iyyar PDP ta dakatad da harkokin yakin neman zaben shugaban kasa saboda babban maigida Jirgin yakin neman zaben PDP ya fara ne daga jihar Akwa Ibom a farkon watan Oktoba, 2022.
Hukumar INEC ta dage takunkumin fara yakin neman zabe tun ranar 28 ga Satumba.
Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP ta sanar da dakatar da yawon yakin neman zabe saboda dan takararta, Atiku Abubakar, ya tafi Amurka.
A jawabin da Diraktan harkokin kwamitin, Umar Bature, ya fitar, ya bayyana cewa an dakatad da ziyarar da akayi niyyar yi zuwa jihohin Ondo, Kebbi, Ekiti da Bayelsa, rahoton Punch.
An dage su zuwa wani lokacin daban. Yace: “Muna mai sanar da dukkan mambobin PCO cewa sakamakon tafiyan dan takaranmu zuwa Amurka, an dakatad da yakin neman zaben da aka shirya a Ondo, Kebbi, Ekiti da Bayelsa.”
“Za’a sanar da sabbin ranakun tarukan. Muna bada hakuri.”
Legit Hausa ta kawo muku labarin cewa Dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, ya dira birnin Washington D.C don yakin neman zaben.
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya samu rakiyar tsohon shugaban majalisa, Bukola Saraki, Sanata Dino Melaye, Phrank Shuaibu.
Sauran sune gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal; shugaban marasa rinjaye a majalisa Ndudi Elumelu; tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha; da Imasugbon.
Hakazalika akwai mammalakin gidan talabijin na AIT, Cif Raymond Dokpesi, Osita Chidoka, da sauran su.
A wani labarin, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya rufe babban ofishin jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar.
A cewar Sahara Reporters, rufe ofishin na cikin shirin na Gwamna Bello don tsayar da kamfen din Natasha Akpoti da ke takarar sanata a jihar.
Akpoti na takarar kujerar sanata ne a na mazabar Kogi Central a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party, SDP, a 2019. A shekarar 2019, ta yi takarar kujerar gwamna a jihar, ta fafata tare da Bello.
A Mayu, Akpoti ta ci zaben fidda gwani na Kogi Central a 2023, za ta fafata da Abubakar Ohere na APC da wasu.
Source;legithausang