Jam’iyyar APC zata tara dukkan yan takara a zaben fidda gwani ciki kuwa harda mataimakin shugaban kasan Yemi Osinbanjo don hada kai wajen ganin Tinubu ya ci zabe.
Tinubu ya lallasa wadannan yan takara a zaben fidda gwanin APC yayinda ya samu kuri’u 1,271.
Hukumar INEC zata gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya ranar 28 ga Febrairu, 2023.
Mutum 22 da sukayi Fom din N100m na takara a zaben fidda gwanin shugaban kasa karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zasu gana don hada kai wa dan takara, Asiwaju Bola Tinubu.
TheNation ta ruwaito cewa an shirya wannan zama ta musamman ranar Laraba mai zuwa don tattauna yadda Tinubu zai lashe zaben 2023.
Tinubu da Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, yayi a Damataru. Daya daga cikin yan takaran a jawabin da ofishin yada labaran sa ya fitar, yace za’a yi wannan zama ne a Abuja.
A cewar jawabin: “Wannan gayyata ta musamman zuwa zaman dukkan yan takaran shugaban kasa na APC wanda za’ayi a Transcorp Hilton Abuja, ranar Laraba, 31 ga Agusta 2022 misalin karfe 2, za’a tattauna hanyoyin yakin neman zaben da za’a bi wajen hada kan kowa don magance matsalolin kasarmu.”
Wadanda ake sa ran zasu halarci zaman sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, tsohon Ministan Kimiya Ognonnaya Onu, tsohon karamin ministan Ilimi Emeka Nwajuiba da tsohon ministan Neja Delta, Godswill Akpabio.
Hakazalika akwai gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, gwamnan Ebonyi Dave Umahi, gwamnan Jigawa Abubakar Badaru, gwamnan Cross River Ben ayade, gwamnan Ekiti Kayode Fayemi da tsohon gwamnan Zamfara Ahmad Sani Yarima.
Sauran sune Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, Sanata Ibikunle Amosun, Sanata Ajayi Borrofice, tsohon Kakakin majalisa Dimeji Bankole, Fasto Tunde Bakare, Fasto Nicholas Felix, Ikeobasi Mokelu, Tein Jack-Rich da Mrs Uju Ken-Ohanenye.
Zaku tuna cewa Tinubu ya lallasa wadannan yan takara a zaben fidda gwanin APC yayinda ya samu kuri’u 1,271.
Wanda ya zo na biyu shine Amaechi wanda ya samu kuri’u 316, sannan Osinbajo mai kuri’u 235.
A wani labarin kuwa, Kashim Shettima wanda shi ne ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa a APC, yace zai maida hankali ga tsaro idan suka kafa gwamnati.
Premium Times tace Sanata Kashim Shettima ya sha alwashin idan suka yi nasara a zaben 2023, zai kula da sha’anin tsaro domin kawo zaman lafiya.
Tsohon gwamnan na Borno ya bayyana wannan a wajen babban taron NBA na kasa da aka yi a Legas, inda ya gabatar da jawabi a gaban Lauyoyi.
Shettima ya fadawa mahalarta zaman da aka yi a farkon makon nan cewa jagoranci jami’an tsaro wajen ganin an samu zaman lafiya a Najeriya.
Source: LEGITHAUSA