Adam Oshiomhole, jigon jam’iyyar APC, ya ce har yanzu babu alamun cewa Atiku zai ci zaben A cewarsa, rikicin jam’iyyar ta PDP babban nakasu ne ga takarar shugaban kasar Atiku.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa jam’iyyar All Progressives Congress, APC ne zai ci zabe.
Legit.ng ta rahoto cewa Kwamared Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Edo ne ya yi wannan hasashen a ranar Juma’a 18 ga watan Nuwamba a Abuja.
Tsohon shugaban jam’iyyar ta APC na kasa ya ce kurakurai da dama da dan takarar shugaban kasar na PDP, Atiku Abubakar ya tafka za su bawa Tinubu damar yin nasara.
A Ji A APC Ya Magantu Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai bayan ganawar sirri da shugaban kasa a Abuja.
Ya yi imanin cewa Atiku ya tafka kura-kurai da dama da za su bawa Tinubu damar yin nasara a babban zaben shugaban kasar na 2023.
A cewarsa, Atiku ya rage wa jam’iyyar ta hamayya damar samun nasara ta hanyar fusata wadanda ya kamata su zama jagororin kamfen dinsa.
Ya bayyana imaninsa cewa dan takarar shugaban kasar na APC zai yi nasara. Gwamnonin APC 23 na tare da Jagaban Oshiomhole ya kara da cewa gwamnonin APC 23 suna aiki tukuru don ganin nasarar Tinubu a babban zaben na 2023, yayin da gwamnoni bakwai kawai ke tare da Atiku, rahoton Sahara Reporters.
Wani sashi na kalamansa: “Idan ta min tambaya yadda muke, zan ce komai na tafiya daidai.
Yayin da dayan na fama da gwamnoni biyar da suka juya masa baya, za ka lura muna da gwamnoni 23.
“Yanzu idan ka kara biyar kan 23, ba wai ina cewa suna tare da mu bane, amma muna da 23 da biyar, ina ganin hakan 28 kenan.
Idan ka cire 28 daga 36, saura gwamnoni takwas, bakwai ma saboda dayan yana APGA ne. ”
Don haka, yayin da yana da gwamnoni bakwai da ke masa aiki, muna da 23 da ke mana aiki, kuma akwai biyar da su yi wa kowa aiki. Idan kana zabe, lokacin da na ke ILO, za ka zabi wani, ko zabi abokin hammaya ko kin zabe. Kin zabe daidai ya ke da zaben abokin hamayya.
Don haka, duk yadda ka kalli abin, kamfen din mu na tafiya lafiya. Sakon ya fito karara. Ba zai iya fin hakan alheri ba.”