Diraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mr Bayo Onanuga, ya sake caccakan makusantan Shugaba Buhari.
Onanuga ya bayyana Ministan Shari’a kuma Antoni Janar, Abubakar Malami, a matsayin makiyi al’ummar Najeriya. Ya kwatanta shi da Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Mr Godwin Emefiele.
Ya bayyana hakan ne a dan gajeren tsokacin da yayi a shafinsa na Tuwita inda yake martani kan bukatar da Malami ya shigar kotun koli biyo bayan hukuncin da ta yanke ranar Laraba.
A cewarsa: “Abubakar Malami ma makiyi al’umma ne kamar Emefiele.”
A wani labarin na daban yayin da ya rage saura kasa da mako biyu a gudanar da zaben shugaban kasa na 2023, ‘yan Nijeriya suna fuskantar matsin canjin kudi da man fetur a karkashin gwamnatin da jam’iyyar APC take jagoranta.
Idan za a iya tunawa a watan Nuwambar 2022, an samu dogayen layuka a gidajen mai a fadin kasar nan sakamakon rashin samun man fetur a wasu gidajen mai, yayin da wadanda ke da man suka sayar da nasu a kan naira 240, wanda ya karu da naira 85 a farashin da kamfanin main a kasa (NNPC) ya amince a kan a sayar da man kan naira 165.
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Nijeriya (IPMAN) ta danganta karin farashin da aka samu kan karin kudin man a rubun sayar da man daga naira 148 zuwa 200 kan kowacce lita.
A cewar shugaban gudanarwa na kungiyar IPMAN, Mike Osatuyi “Ba kamar yadda a baya ‘ya’yan kungiyarmu ke sayan man kan naira 148 kan kowacce lit aba, a halin yanzu suna sayan kowacce lita kan naira 200. Ba zai yi wuya su sayar da man fetur a kan naira 165 kan kowacce lita kamar yadda aka kayyade.
“A halin yanzu mambobin kungiyarmu suna matukar shan wahala wajen samun man. Haka kuma ‘yan kasuwan suna kashe makudan kudade wajen kai man zuwa sassa daban-daban na kasar nan saboda tsadar man dizil, inda a halin yanzu ana sayar da kowacce lita daya ta dizil kan naira 800.
A hannu guda kuma, ‘yan Nijeriya ba su farfado daga matsalar karancin man fetur ba, sai babban bankin Nijeriya (CBN) ya sauya fasalin kudi tare da bayar da wa’adin ranar 31 ga Junairu za a daina amsar tsofaffin takardun kudi na naira 200, 500 da kuma 1,000.
CBN ya sanar da shirin sake fasalin wasu takardun kudaden ne a ranar 26 ga Oktoban 2022, da nufin rage hauhawar farashin kayayyaki da hana fasa kwaurin kudin banki da kuma rage zirga-zirgan kudade.
A ranar 23 ga watan Nuwamban 2022, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudade, wanda aka gabatar wa jama’a a ranar 15 ga Disambar 2022.
Kwanaki kadan gabanin wa’adin farko na ranar 31 ga Janairu ya kare, an ga jerin layuka a na’urar cire kudi (ATIM) na bankuna daban-daban da ke Nijeriya wajen neman cire kudin sabbin kudade, yayin da wasu bankunan suke rufe na’urar ATM dinsu saboda dalilin cire kude.
Rashin fitar da sabbin takardun kudade da bankuna ke kin yi ya sa lamarin ya kara ta’azzara, domin a cewar rahotanni, da yawa daga cikinsu sun ci gaba da fitar da tsofaffin takardun kudaden ta na’urar ATM kuma tsawan makonni da fitowar sabbin kudaden ba a bayar da su a cikin bankuna.
Duk da tsawaita wa’adin daina amsar tsofaffin takardun kudaden da CBN ya yi da kwanaki 10 tare da bayar da umurni ga bankuna kan yadda za a samar da sabbin takardun kudaden da aka sauya wa fasali ga ‘yan Nijeriya, amma al’umma kasar nan na cikin firgici saboda rashin isassun sabbin kudaden a hannun jama’a.
“Zan iya bayyana muku cewa kullum CBN ya bai wa bankuna sabbin kudade. Kamar yadda nake magana a halin yanzu, bankuna sun amshi sabbin kudade daga CBN.
“Ina tabbatar muku da cewa muna rokon bankuna kasuwanci da su zo su karbi sabbin kudade daga CBN. Muna da wadannan sabbin takardun kudade a rumbun ajiyarmu, kuma muna jiran bankuna su zo su karbe su,” in ji Daraktan sashen shari’a na CBN, Mista Kofo Salam-Alada, a wani shirin wayar da kan jama’a na kauyen Kwamfuta da ke Ikeja a Jihar Legas a ranar 19 ga Janairu.
Rashin samun sabbin kudaden ya yi matukar illata harkokin kasuwanci, musamman ma bangaren da ake hada-hada da tsabar kudade wajen gudanar da harkokin kasuwanci.
Jam’iyyar APC tana ganin cewa an kawo wadannan tsarin ne domin a hana ta cin zabe.
Mai Magana da yawun dan takarar shugaban kasa na APC, Dakta Jose Onoh ya siffanta tsarin sauya takardun kudade da gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele ya kawo a matsayin huce haushi kan siyasa bayan da ya gaza samun tikitin takarar shugaban kasa.
Onog ya kara da cewa sake fasalin naira ba wai tsatin jam’iyyar APC ba ne, illa ce ta Emefiele wanda a halin yanzu ke kawo cikas ga tattalin arzikin kasa, inda ya bayar da shawarar cewa kasar ta yi koyi da tsarin kasar Ingila na canjin kudi a hankali har na tsawon watanni 12 a kalla.
Onoh ya jaddada cewa bai kamata a daidai lokacin zabe a sauya fasalin takardun kudade, kuma wannan muguwar manufar Emefiele na hukunta ‘yan Nijeriya saboda ya gaza samun takarar shugaban kasa.
Ya bayar da misalign irin tashin hankula da ‘yan Nijeriya suka fada sakamakon karancin kudade wadanda suka hada da zanga-zanga, sayar da sabbin kudade ba bisa ka’ida ba, tilastawan ‘yan ta’adda kan samun sabbin kudaden da kuma sauran matsaloli da suka shafi zamantakewa.
Ya ce abin takaici ne yadda gwamnatin Nijeriya ta nada wanda bai cancanta ya tafiyartar da harkokin kudade ba, kuma babban kuskure ne tun lokacin da gwamnan CBN ya shiga siyasa.
A cerwarsa, ko kadan bai kamata a bar Emefiele ya koma bakin aiki ba bayan ya gaza samun takarar shugaban kasa, yana jin haushin rashin nasara da ya yi wanda ya zabi ya huce haushinsa kan daukacin al’ummar Nijeriya.
Onoh ya yi gargadin cewa manufar sake fasalin kudin naira na CBN shi ne, ya haifar da tarzoma cikin jama’a, yana mai jaddada cewa ya kamata Emefiele ya bar ofis ne a daidai lokacin da ya nuna sha’awar zama dan takarar shugaban kasa.
A cikin makon da ya gabata ne, Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufa’i ya bayyana cewa akwai wasu daga cikin fadar shugaban kasa suna yin kutungwila ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu wajen ganin bai ci zaben 2023 ba.
El-Rufa’i ya bayyana hakan ne lokacin da yake fira da BBC Hausa, wanda ya ce sauya fasalin takardun kudi abu ne mai kyau amma bai kamata a gudanar da shi a daidai lokacimn da ake fusukantar zabe ba. Ya ce an yi hakan ne saboda a saka kiyayya a tsakanin ‘yan Nijeriya da jam’iyyar APC.
Sai dai kuma masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC sun goyi bayan gwamna el-Rufai na ikirarin akwai wadanda suke zagaye da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ba sa kaunar Tinubu.
Tun a shekarun da suka gabata ne, Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta sanar wa ‘yan Nijeriya cewa akwai kabal a suka kewaye mijinta wadanda suka hana ruwa gudu.
Shugaban tawagar masu ruwa da tsaki na APC, Dominic Alancha ya tabbatar da cewa akwai wadansu mutane da ke kewaye da shugaban kasa suna hana ruwa gudu ga nasarar jam’iyyar.
Haka kuma Alancha ya zargi kwamitin gudanarwa na jam’iyyar kan kin bayyana wa sauran mambobin jam’iyyar bayanan kudade.
Alancha ya koka kan yadda ‘ya’yan jam’iyyarnke sauya sheka zuwa jam’iyyun adawa tun bayan zaben fitar da gwani na 2022, yayin da manyan masu ruwa da tdsaki suka yi watsi da su.
Masana harkokin siyasa suna ganin wadannan lamura za su iya kawo wa jam’iyyar APC cikas a zaben 2023. A mahangar masanan, matsin canjin kudi da karancin man fetur suna iya goga wa APC bakin jini na rasa magoya baya.
Source:LeadershipHausa