Kwamishinar masana’antu a jihar Abiya, Uwaoma Olawengwa, ta yi murabus daga kan muƙaminta kana ta sanar da ficewa daga PDP.
Olawengwa ta bayyana cewa dalilin ɗaukar matakin sabule hannunta daga gwamnati sirri ne kuma ita kaɗai ya shafa.
Gwamnan Abiya, Okezie Ikpeazu, na ɗaya daga cikin makusantan gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas
Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, ɗaya daga cikin gwamnonin G5 dake marawa Wike baya, ya rasa kwamishinarsa ta koma jam’iyyar APGA.
A rahoton da jaridar Tribune ta tattaro, kwamishinar masana’antu ta jihar Abiya, Uwaoma Olawenga, ta yi murabus daga muƙaminta a majalisar zartaswan Ikpeazu.
Da take zantawa da manema labarai a Umuahia, babban birnin jihar, Olawengwa, ta bayyana cewa ta ɗauki matakin murabus ne saboda wasu dalilai na ƙashin kanta.
Tsohuwar kwamishinar tace ta kuma yanke komawa jam’iyyar APGA ba don komai ba sai don ta zama ɗaya daga, “tawagar cigaba da zata kawo sauyi a Abiya.”
Gwamna Arewa Ya Sake Tayar da Ƙura a PDP Kan Wanda Ya Kamata ‘Yan Najeriya Su Zaɓa a 2023
Ta kuma sanar da cewa da kanta ta rubuta takardar sauka daga muƙaminta kuma ta miƙa wa gwamna Ikpeazu ba tare da ɗan aike ba.
A jawabinta, Olawengwa ta ce:
“Dalilin da yasa na bar PDP sirri ne na karan kaina amma abinda ya fi muhimmanci shi ne na sauka daga mukamina a gwamnati domin na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APGA.”
“Na shiga APGA ne saboda ina da yakinin idan muka haɗa tawagar nagartattu masu son ci gaba zamu sauya akalar jihar mu.”
Daga nan sai tsohuwar kwamishinar masana’antun ta yaba wa jam’iyyar APGA bisa zakulo Farfesa Gregory a matsayin ɗan takarar gwamnan Abiya a zaɓe mai zuwa.
Ta ƙara da cewa Abiya zata ga cigaba bila adadin idan har mutane suka yi wayon kaɗa masa kuri’unsu ya zama gwamna a 2023.
Ana hasashen dai murabus din kwamishinar da kuma shigarta jam’iyyar APGA ka iya kawo cikas ga damar PDP na cigaba da mulkin Abiya a 2023.
A wani labarin kuma Gwamna Ortom na tsagin Wike a PDP ya faɗa wa mutanen Benuwai wanda ya kamata su zaba a 2023
Da yake jawabi a bayan sa hannu a kasafin kuɗin 2023, Ortom ya shawarci mazauna jihar da su zabi nagartattun mutane masu amama su guje wa sak.
A cewarsa da yawan mutane na tsammanin shekarar 2023 mai zuwa zata zo a abubuwa masu kyau da zai share masu hawaye.