Wani dan kudu, Maxwell Nwadike, ya yi ikirarin cewa ana yi wa Bola Tinubu matsin lamba ya ajiye takarar shugaban kasarsa.
Nwadike cikin wani rubutu da ya yi a Twitter, ranar 25 ga watan Agusta, ya yi ikirarin cewa matsin lamban na zuwa ne daga likitan Tinubu a kasar Faransa.
Amma, Joe Igbokwe, na hannun daman tsohon gwamnan na Legas ya karyata ikirarin Nwadike kuma aka ce labarin kanzon kurege ne.
Joe Igbokwe, daya cikin na hannun daman Asiwaju Bola Tinubu, ya yi martani kan ikirarin da wani Maxwell Nwadike ya yi na cewe likitan dan takarar shugaban kasa na APC ya shawarce shi ya ajiye takararsa na 2023.
A cewar Nwadike a wani rubutun da ya yi a Twitter a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, ya yi ikirarin cewa yanayin lafiyar Tinubu a halin yanzu ne yasa likitansa ya bashi wannan shawarar.
Da ya ke magana kan ikirarin, Igbokwe a wani rubutu da ya yi a Facebook a ranar Juma’a, 26 ga watan Agusta, ya bayyana batun a matsayin tsantsagwaran karya.
Igbokwe ya fayyace cewa “kareraki, labaran bogi, farfaganda, zagi, bita da kulli da sauransu ba za su taimakawa kowa cin zaben shugaban kasa na 2023 ba.”
Ya ce abin da kawai zai iya taimakawa mutum cin zabe sune ‘ayyukan kirki da mutum ya yi a baya, kwarewa, ilimi, zumunci, kusantar talakawa, sanin mutane a kasa da kasashen waje, magoya baya da abota da aka gina na tsawon shekaru’.
Igbokwe ya kammala rubutunsa na Facebook da cewa: “Asiwaju ya dade yana aiki kuma yana shirin darewa kujerar shugaban kasa tun kafin shekarar 1993 …”.
Olusegun Obasanjo Ya Ce Bangaren Tinubu Sun Masa ‘Sharri’ A wani rahoton, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gargadi wasu magoya bayan Asiwaju Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Daily Trust ta rahoto.
Tinubu da wasu jiga-jigan APC sun ziyarci Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, babban binrin Jihar Ogun, a ranar Laraba.
Cikin wadanda suka yi wa Tinubu rakiya akwai tsaffin gwamnonin jihar Ogun, Olusegun Osoba da Otunba Gbenga Daniel, dan kasuwa kuma tsohon shugaban riko na APC, Cif Bisi Akande da Kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila.
Source: LEGITHAUSA