Malam Nuhu Ribadu ya ganin zaben shugaban kasa mai zuwa zai zo wa jam’iyyar APC da sauki.
Tsohon shugaban hukumar EFCC yace APC za ta ci zabe saboda sun fi kowa ‘dan takara mai kyau.
Ribadu ya na ganin tallata Bola Tinubu zai yi sauki saboda kwarewarsa, sunansa da sanin aikin sa.
Tsohon shugaban hukumar EFCC na kasa, Nuhu Ribadu yace a cikin ruwan sanyi, Asiwaju Bola Tinubu za iyi nasara a zaben shugaban kasa.
Vanguard a wani rahoto da ta fitar a ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamba 2022, tace Mallam Nuhu Ribadu ya hango galabar jam’iyyar APC mai mulki.
Nuhu Ribadu wanda shi Darektan hulda da masu ruwa da tsaki a kwamitin neman zaben shugaban kasa na APC ya yi wannan bayani a garin Abuja.
Tsohon ‘dan sandan yake cewa Asiwaju Bola Tinubu zai yi nasara, amma duk da haka bai kamata APC ta raina ‘yan takaran jam’iyyar hamayya ba.
An rahoto Ribadu yana cewa inda jam’iyyar APC mai mulki ta taki sa’a shi ne, ‘dan takaransu yana da saukin tallatawa a kan ragowar masu takaran.
Abin da Ribadu yace a kan Tinubu “Mun yi sa’a, aikinmu ya zo mana da sauki.
Mu ke da ‘dan takaran da ya fi kowane dadin tallatawa a kasuwa. Babu ‘dan takaran da ya fi na mu.
“Asiwaju Tinubu mutum ne da ya cin ma nasarorin rayuwa, kwararren shugaba kuma gawurtaccen ‘dan siyasa ne.
An san irin abin da ya yi a baya.
Sannan kuma ya san kan-aiki, ba a kan mulki zai gano dawar garin ba. Yana kuma da ‘dinbin mutane, jama’a da abokai a ko ina a Najeriya.
Hakan ya sa shiga wurare ba zai yi mana wahala sosai ba.
da mu raina abokan adawa, muyi aiki domin a samu tazara sosai. Tribune tace tsohon shugaban APC na kasa, Cif Bisi Akande ya halarci bikin kaddamar da kwamitin, yace ya gamsu da rawan gwamnati mai-ci.
APC tayi kuskure – Kwankwaso Duk da kwanaki ya yabi Asiwaju Bola Tinubu, amma da ya ziyarci Ebonyi domin kamfe, an ji labari Rabiu Musa Kwankwaso yace APC tayi kuskure.
‘Dan takaran na NNPP yana ganin Bola Tinubu a matsayin wanda zai kawowa jam’iyyar APC nasara a zaben 2023 ba zabi mai kyau ba ne da aka yi.
Source:LEGITHAUSA