Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC ta dage lokacin cigaba da jigilar fasinjoji a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, sufurin da ta dakatar tun bayan harin da ‘yan bindiga suka kai kan daruruwan fasinjoji a ranar 28 ga watan Maris.
A baya dai hukumar ta NRC ta tsayar da ranar Litinin 23 ga watan Mayu ne domin cigaba da sufuri, amma ‘yan uwan wadanda ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su suka ki amincewa da matakin, la’akari da cewar har yanzu ba a ceto ‘yan uwansu da aka yi garkuwa da su ba.
A wani mataki da wasu ke dangantawa da amsa bukatun masu koken ne kuma hukumar ta NRC ta hannun kakinta Mahmud Yakubu ta sanar da dage ci gaba da jigilar da ta shirya komawa, ba kuma tare da tsayar da sabuwar rana ba.
A baya bayan nan mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya ce ana ci gaba da tattaunawa don ganin an sako mutanen da ‘yan bindiga suka sace a harin da suka kaiwa jirgin kasan da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga Abuja.
Akalla mutane 9 aka tabbatar sun rasa rayukansu wasu sama da 20 kuma suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga, sai kuma sace fasinjoji da dama a lokacin harin a watan Maris.