Kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, ya ce dan takararta na shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso zai kayar da abokan hamayyarsa da kuri’u miliyan uku a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kwamitin yakin neman zaben NNPP ga bayyana hakan ne a ranar Litinin cikin wata sanarwa da Cif Precious Elekima, Kodinetan Kudu Maso Kudu na kwamitin ya fitar.
A cewar kwamitin, Rabi’u Kwankwaso zai yi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa domin tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya za su iya zabar shugabanni masu nagarta da kima.
Kwamitin na Kwankwaso ya kuma ce ba gaskiya ba ne cewa jam’iyyar za ta mara wa wani dan takara baya.
Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya nagari da su zabi mutumin da ya shahara da amana da gaskiya wanda zai ceto Nijeriya.
A wani labarin na daban kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben Mista Biodun Oyebanji, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Ekiti da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yunin 2022.
Kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke kusan ranar Talata, ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP da ya sha kaye, Cif Segun Oni, ya shigar tare da warware dukkan batutuwa hudu da suka shafi wanda ya shigar da kara.
A cikin hukuncin watsi da daukaka karar, kotun ta kuma bukaci biyan kudi Naira 200,000 kan wadanda suka shigar da kara.
A hukuncin da shugaban kwamitin daukaka kara mai mutane uku, Mai shari’a Hamma Barka, ya yanke, kotun ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke a ranar 29 ga watan Disamba, 2022 wanda ke kalubalantar Oyebanji a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kotun ta amince da kotun cewa Oyebanji ya cancanci tsayawa takarar gwamna bayan an tantance shi a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a Jihar Ekiti a ranar 27 ga watan Janairu.
Source:LegitHausa